Buhari ya fi son Kudu maso Yamma fiye da sauran yankuna a gwamnatin sa – Adebayo Shittu

Buhari ya fi son Kudu maso Yamma fiye da sauran yankuna a gwamnatin sa – Adebayo Shittu

Ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya bayyana cewa yankin Kudu maso Yamma sun amfana fiye da sauran yankuna a kasar daga gwamnati mai ci na shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Buhari ya fi son Kudu maso Yamma fiye da sauran yankuna a gwamnatin sa – Adebayo Shittu

A wata hira tare da jaridar Vanguard, ministan yayi bayanin cewa dukka jihohin Kudu maso Yamma na da Minista sai dai wata jiha guda.

A cewar Shittu, “Nazo na gamsu da cewa, dukkan yankunan da suka amfana daga gwamnatin Buhari, a bayan amfanar da Kudu maso yamma ta yi yake kuma zan fada maku dalili.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Osinbajo zai kai ziyara jihar Edo a safiyar nan

“Dukka jihohi shidda dake Kudu maso Yamma na da minista baya ga jiha guda daya. Ba wai ministoci kawai ba, a’a ministocin manyan ma’aikatu.

“Na kasance ministan sadarwa, sama da shekara daya da ya wuce, na bayar da gudunmuwa fiye da kaso koma cikin dari na giddidiga (GDP). Muna da minister mai matsayi uku a Fashola (SAN), wanda ke kula da wutan lantarki, ayyuka da kuma gidaje.

“Muna da minstan lafiya a Farfesa Adewole sannan kuma kun san yadda minstan nan ke da muhimmanci. Sannan kuma, muna da ministan ma’adinai, wanda shine mabudin tattalin arziki na kasa kamar Najeriya sannan kuma Dr. Kayode Fayemi daga Ekiti na kula da guda.

“Jihar Ondo ne kawai keda ministan jiha. Sannan jihar Ogun na da ministan kudi Misis Kemi Adeosun.

“Ina nufin ban san ko wani yankuna, wanda ke da wannan damar ba. Don haka, ta fannin rashin banbamci, Kudu maso yamma sun fi amfana. Bai taba faruwa ba a tarihin kasar nan inda zaka samu gwamnatin tarayya da ministoci da dama daga kasar yarbawa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa

Sarkin Musulmi ya koka da karuwar shan Kodin a cikin matasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel