Anfani 5 da man kwakwa yake yi a jikin dan adam

Anfani 5 da man kwakwa yake yi a jikin dan adam

Kawo yanzu dai wajen bincike sama da 1,500 aka gudanar a kan man kwakwa da kuma anfanin sa a jikin bil'adama. Akwai ma masu hasashen cewa yafi duk wani abinci dake duniyar nan anfani.

Anfani 5 da man kwakwa yake yi a jikin dan adam (Karanata)
Anfani 5 da man kwakwa yake yi a jikin dan adam (Karanata)

Bincike dai ya nuna cewa kusan kashi 62% na man kwakwar yana kunshe ne da wasu sinadarai masu matukar anfanin a jin mutane.

Ga dai wasu daga cikin anfanonin sa nan da muka kalato maku:

1. Yana hana ciyon zuciya da kuma hawan jini

Kasantuwar man kwakwa nada dauke da sinadarin kitse marar nauyi wanda kuma yake da matukar anfani, shan man kwakwar yana hana mutum kamuwa da cututtuka ire-iren su ciwon zuciya da kuma hawan jini.

2. Yana maganin ciwon koda da kuma hanta

Bincike ya nuna cewa man kwakwa yana wanke koda don haka kuma yakan magance dukkan wasu cututtuka da suka shafi kodar. Sabon bincike kuma har ila yau ya bayyana cewa yana kare hanta daga cuttutuka da dama.

Anfani 5 da man kwakwa yake yi a jikin dan adam (Karanata)
Anfani 5 da man kwakwa yake yi a jikin dan adam (Karanata)

3. Yana kare mutum daga cutar daji (Kansa)

Sabbin bincike da ake ci gaba da yi a kan man kwakwar ya nuna cewa yana maganin cutar daji wadda a yanzu ta zama kusan ruwan dare. An gano cewa wasu sinadaren dake cikin sa suna hana kamuwa da cutar.

4. Man kwakwa yana kara karfin garkuwar jiki

Kasantuwar man kwakwa yana kunshe da sinadarin 'lauric acid' wanda bicike ya tabbatar da yana maganin cututtuka da dama sannan kuma yana kara karfin garkuwar jiki.

5. Man kwakwa yana maganin gyambon ciki

Haka zalika bincike ya tabbatar da cewa man kwakwa yana taimakawa wajen maganin gyambon ciki saboda yana kunshe da sinadaran Maganesium da Calciom kai har ma da wasu nau'oi na Vitamins.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kalli bidiyon kasa kan ciwon zuciya:

Asali: Legit.ng

Online view pixel