Shin za a hana ‘Achaba’ a Najeriya ne?

Shin za a hana ‘Achaba’ a Najeriya ne?

– Ministan sufuri yace bai dace Gwamnoni suyi kokarin hana Achaba ba

– Rotimi Amaechi yace hana ‘Achaba’ zai kawo babbar matsala a Najeriya

– Gwamnoni dai na kokarin hana hawa babur da 'keke napep'

Shin za a hana ‘Achaba’ a Najeriya ne?

Shin za a hana ‘Achaba’ a Najeriya ne?

Ministan sufuri na kasa Rotimi Amaechi yace bai dace Gwamnoni suyi kokarin hana Achaba ba. Amaechi yace hakan zai kawo matsala ne kurum ga tattalin arzikin kasar don haka ya gargadi Gwamnonin kasar da wannan kudiri.

Rotimi Amaechi ya bayyana haka ne ga hukumar dillacin labarai watau NAN wajen taron kungiyar masu ‘keke napep’ da babur na kasa. Amaechi yayi wa Gwamnoni kashedi cewa kul aka hana Jama’a hawa achaba domin zai kara radadin da ake ciki na tattalin arziki.

KU KARANTA: Matukin jirgin sama ya mutu a bakin aiki

Shin za a hana ‘Achaba’ a Najeriya ne?

Shin za a hana ‘Achaba’ a Najeriya ne?

Ministan yace abin da ya kamata ayi shi ne a koyawa ‘yan achaban da sauran matuka aiki da bin dokar hanya saboda irin yawan haduran da ake samu a a fadin kasar. Amaechi yace masu babur suna da amfani don kuwa ba ko ina mota ke iya ratsawa ba.

Sannan kuma dai fadar shugaban kasa tace Najeriya ta kama hanyar fita daga radadin tattalin arzikin da ake ciki. Najeriya dai na fama da durkushewar tattalin arziki tun bara bayan farashin mai ya rushe amma yanzu alkaluman sun nuna an fara kama hanyar farfadowa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel