Subhanallah! Mota ta fada cikin tekun jihar Legas

Subhanallah! Mota ta fada cikin tekun jihar Legas

Akalla mutane 3 sun hallaka a wata hadari da ya auku da safiyar yau Juma’a yayinda wata babbar mota ta kubce daga kan hanya kuma silliye cikin tekun jihar Legas.

Subhanallah! Mota ta fada cikin tekun jihar Legas

Subhanallah! Mota ta fada cikin tekun jihar Legas

Hadarin ya faru ne misalin karfe 3:23 na dare a Owode Elede, Mile 12 area, Ikorodu, jihar Legas.

Motar mai lamba Anambra GDD 386 YE, na kamfanin GUO Transport Service Co. LTD wacce take zuwa daga Maza-Maza Aba, jihar Abiya.

Game da cewar hukumar bada agaji na gaggawa ta jihar Legas, LASEMA, fasinjoji 59 ne ke cikin motan. 23 sun jikkata kuma an kula da su a take.

KU KARANTA: Martaban mace a addinin Musulunci

Kakakin hukumar LASEMA , Kehinde Adebayo, ya kara da cewa 9 daga cikin wadanda suka jikkata an kaisu asibitin kula da hadari da ke Toll Gate domin jinya.

Amma, fasinjoji 3 sun rasa rayukansu a take. Wanda ya kunshi kwandaston motan da wasu guda 2 da ba’ a game ba har yanzu.

An ciro gawarsu daga cikin tekun kuma an mika ga ofishin yan sandan Owode.

Manajan LASEMA , Adesina Tiamiyiu yace za’ a gudanar a bincike cikin al’amarin kuma anyi kira ga direbobi masu tukin dare su daina gudu.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel