‘Sama da yan fansho miliyan 1 ne suka mutu a Kwara suna jiran hakkinsu’ – inji Kungiyar Fansho

‘Sama da yan fansho miliyan 1 ne suka mutu a Kwara suna jiran hakkinsu’ – inji Kungiyar Fansho

Kungiyar yan fansho ta kasa (NUP) ta bayyana a ranar Alhamis 16 ga watan Feburairu cewar yan fansho 1, 126, 000 ne suka mutu a jihar Kwara ba tare da biyansu hakkokinsu ba.

Kungiyar ta zargi gwamnatin jihar da sabbaba mutuwar yayan kungiyar tasu, musamman yan fanshon kananan hukumomin jihar.

Jaridar Daily Post ta ruwaito kungiyar tana ikirarin sama da yayan kungiyar 1000 sun mutu ne sakamakon rashin kudin asibiti.

‘Sama da yan fansho miliyan 1 ne suka mutu a Kwara suna jiran hakkinsu’ – inji Kungiyar Fansho

‘Sama da yan fansho miliyan 1 ne suka mutu a Kwara suna jiran hakkinsu’ – inji Kungiyar Fansho

Shugaban kungiyar Isiaka Akanbi ne ya shaida haka yayin taron manema labaru a garin Ilorin, inda ya bada sunayen yan fansho hudu da suka rasu a karamar hukumar Ifelodun, sune: Garba Okoye, N.S Alabi, mai shekaru 72, Mrs. John mai shekaru 62, sai kuma Alashi mai shekaru 68.

Sa’annan ya kara da cewa yan fansho su 6000 wadanda tsofaffin malaman makarantun sakandari da firamari ne suna bin gwamnatin jihar sama da Naira biliyan 5 kudin gama aiki.

Akanbi yace tun shekaru 10 da suka gabata ba’a sake biyan fansho a jihar, inda ya zargi gwamnatin jihar da kin biyan hakkokin yan fanshon ba tare da wani kwakkwaran dalili ba. Sa’anan yace gwamnatin taki yi ma ma’aikata karin karancin albashin da aka yanke tun a shekarar 2010.

Daga karshe, Akanbi yayi kira ga shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki daya sanya baki a cikin matsalar ta hanyar yi ma gwamna Abdulfatah magana ya biya yan fansho kudinsu ko zasu samu saukin rayuwa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel