Mace ta farko data zagaye ƙasashen duniya 196 a watanni 18

Mace ta farko data zagaye ƙasashen duniya 196 a watanni 18

Wata mata yar shekaru 27 mai suna Cassie De Pecol yar garin Connecticut kasar Amurka ta kafa tarihin kasancewa mace mafi karancin shekaru data fara zagaye kasashen duniya gaba daya, inda ta kai ziyara kasashe 196.

Mace ta farko data zagaye ƙasashen duniya 196 a watanni 18
Mace ta farko data zagaye ƙasashen duniya 196 a watanni 18

Matar ta kwashe watannin 18 da kwanaki 26 tana yin balaguron, hakan ke nuna ta kafa tarihin karancin lokaci na zagaye kasashen duniya. Kuma ta zagaya kasashe 196 ciki har da kasar Taiwan, Kosovo da Palestine.

A yanzu Cassie De Pecol ta fara cike-ciken takardun kundin tarihin duniya don kafa tarihi, Cassie De Pecol ta kashe dala 198, 000 kimanin naira miliyan 99 a kudin jirgi, kuma ta hau jirgi sau 255.

KU KARANTA: Trump ya janye dokar hana musulmai shiga Amurka, zai sauya fasalinta

Mace ta farko data zagaye ƙasashen duniya 196 a watanni 18

Abinka da bature, dayake Cassie De Pecol ta jajirce akan manufarta na lallai sai ta kafa tarihi a zagayen duniya, kuma gashi bata da kudi, amma Cassie De Pecol bata yi kasa a gwiwa ba, inda ta je tayi aikin rainon jarirai, anan ne ta samu ta tara dalan Amurka 10,000, sa’annan ta samu tallafi daga kungiyoyi masu zaman kansu.

Mace ta farko data zagaye ƙasashen duniya 196 a watanni 18

Cassie De Pecol ta fara balaguron ne tun a watan Yulio na shekarar 2015 da tayi ma taken ‘Expedition 196’, inda a ranar 2 ga watan Feburairu ta isa kasar Yemen, kasa ta 196, kuma kasa ta karshe data ziyara, sa’annan kuma tana yin kwanaki 2 zuwa 5 a kowane kasa, kuma ta shuka bishiyoyi a sama da kasashe 50.

Manufar Cassie De Pecol shine ta isar da sakon zaman lafiya a duk fadin duniya ta hanyar saduwa da mutane daban daban a duk fadin duniya, tare da kafa tarihi wajen yin hakan, sa’annan ta dauki tafiyan nata a gaba daya a na’urar daukar hoto.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel