Buhari ya sha alwashin ganin bayan cin hanci da rashawa a Najeriya

Buhari ya sha alwashin ganin bayan cin hanci da rashawa a Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin yakar cin hanci da rashawa gaba daya a kafatanin Najeriya.

Buhari ya bada wannan tabbaci ne a bikin kaddamar da shirin gwamnati na yaki da cin hanci da aka yi ma taken ‘The Value Project’ daya gudana a babban birnin tarayya Abuja.

Buhari yaci alwashin ganin bayan cin hanci da rashawa a Najeriya

Shugaba Buhari ya samu wakilcin ministan Ilimi Farfesa Anthony Anwukah, yace satar kudaden al’umma, da cin hanci da rashawa da sauran ayyukan zamba sune manyan matsalolin da kasar ne ke fuskanta, kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.

KU KARANTA: An samu ɓullar wata annoba a makarantar sakandari a Zamfara

Taron wanda ma’aikatar Ilimi tare da hadin gwiwar wata kungiya mai zaman kanta suka shirya nada manufar samar da sabuwar Najeriya tare da karar da matsalar cin hanci da rashawa a kasar ta hanyar samar da ingantaccen Ilimi da sauya tunanin dalibai a matakin firamari da sakandari a dukkanin jihohin kasar nan.

Shugaban kasa yace “ina tunanin idan dai zamu iya magance matsalar cin hanci da rashawa gabaki daya, toh lallai zamu samar da sabuwar Najeriya yar yayi. Wanda kowa zai yi alfahari da ita.

“A cikin shekara guda da gwamnatin mu ta kwashe, mun yi kokari sosai wajen tabbatar ma kowa cewar sai mun ga bayan cin hanci da rashawa tun kafin ta durkusar da Najeriya.

“Ina da tabbacin ayyukan zamba irin su badakalar kasafin kudi, satar amsa, cin hanci na malamai, kara kudin kwagila, satar kudin al’umma da karbar rashawa sune rabin matsalolin kasar nan.”

Daga nan sai ya bukaci yan Najeriya dasu kasance masu kishin kasa wajen goyon bayan gwamnatin nan a kokarin ta na sauya tunanin yan Najeriya, musamman kananan yara.”

A wani labarin kuma, wata babbar kotun jihar Legas ta halatta ma gwamnatin tarayya kudi naira biliyan 34.9 da aka kwato daga hannun tsohon ministan kula da harkar man fetur Diezani Alison-Madueke, inji rahoton Premium Times.

Mai shari’a Muslim Hassan ya bayyana haka a ranar Alhamis, inda ya halatta ma gwamnatin bayan ya gamsu da jawabin hukumar EFCC dangane da asalin kudin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel