Yan Boko Haram sun kai hari kan jirgin yaki na rundunar sojan sama

Yan Boko Haram sun kai hari kan jirgin yaki na rundunar sojan sama

Yayan kungiyar ta’addanci na Boko Haram sun kai wani mummunar hari kan jirgin saman yakin mallakar rundunar sojan sama a ranar Laraba 15 ga watan Feburairu yayin da jirgin ke sintirin kai kwararrun likitoci sansanin yan gudun hijira dake Gwoza, jihar Barno.

Yan Boko Haram sun kai hari kan jirgin yaki na rundunar sojan sama

Yan Boko Haram sun kai hari kan jirgin yaki na rundunar sojan sama

Kaakakin rundunar sojin sama Gruf Keftin Ayodele Famuyiwa ne ya shaida haka a wata sanarwa daya fitar ranar Alhamis 15 ga watan Feburairu inda yace jirgin yakin kirar Mi-17 ya fuskanci harbi sosai daga yan ta’addan, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai babu wanda ya mutu, face wani jami’in soja daya jikkata. Famuyi yace jirgin ya tashi daga garin Maiduguri kenan a hanyarsa ta zuwa Gwoza don ziyarar aiki kenan ya fara shan wuta daga yan ta’addan.

KU KARANTA: Addinin Musulunci bai yarda da nuna bambamcin launin fata ba

“Duk da haka, matukin jirgin ya sarrafa jirgin yadda ya kamata, kuma mun gudanar da aikin mu ba tare da wani tsaiko ba.

“Ganin haka ne hukumar sojin saman ta tashi wani jirgin yaki na musamman ta aika shi inda aka samu harbe harben don gano yan ta’addan tare da yi musu rubdugun wuta, kuma an samu nasar sakamakon rahoton da ya fito daga sojojin dake kasa sun tabbatar da mutuwar yayan Boko Haram da dama a wajen da lamarin ya faru.

“Za’a iya tuna cewar rundunar sojin kasa tana kai likitoci sansanonin yan gudun hijira a matsayin gudunmuwar ta gare su, kuma ko a jihar Legas ma tayi kwatankwacin wannan.”

A wani labarin kuma, rundunar sojan sama ta kara kaimi wajen yin luguden wuta ga yan ta’adda a kokarinta na ganin ta murkushe ragowar yan Boko Haram da suka rage a wasu sassan dajin Sambisa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel