Trump ya janye dokar hana musulmai shiga Amurka, zai sauya fasalinta

Trump ya janye dokar hana musulmai shiga Amurka, zai sauya fasalinta

A ranar Alhamis, 16 ga watan Feburairu ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya janye daukaka karar da yayi akan hukuncin kotun data yi watsi da bukatarsa na ganin ya hana musulmai matafiya da yan gudun hijira shiga kasar ta Amurka.

Trump ya janye dokar hana musulmai shiga Amurka, zai sauya fasalinta

Trump ya janye dokar hana musulmai shiga Amurka, zai sauya fasalinta

Sai dai shugaban ya sha alwashin sake fasalin dokar don tabbatar da manufarsa.

A baya dai bangaren shari’ar kasar Amurka ta sanar da cewar wannan mataki da Donald Trump ke son dauka yaci karo da tsarin mulkin kasar Amurka.

KU KARANTA: Yadda aka tsige Muduru aka sauya shi da Kusada a matsayin kaakakin majalisa

“A maimakon rikita rikitan shari’a a kotuna, shugaba Trump ya yanke shawarar sauya ma dokar fasali don canza abubuwan da alkalan suke gani kamar yi ma kundin tsarin mulki karan tsaye ne.” a cewar sanarwar.

Idan dai ba’a manta ba, jim kadan bayan darewarsa karagar mulki ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bada umarnin hana musulman daga kasar Syria da waus kasashe guda 6 na yankin Larabawa da Afirka shiga kasar Amurka.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel