Wani ɗan Najeriya yayi takakkiya zuwa Landan don kai ma Buhari sakon ‘Allah ya baka lafiya’

Wani ɗan Najeriya yayi takakkiya zuwa Landan don kai ma Buhari sakon ‘Allah ya baka lafiya’

Wani dan Najeriya Akinjide Ajisafe yayi takakkiya har birnin Landan don aika ma shugaba Buhari sakon ‘Allah ya baka lafiya’ a masaukin Buhari dake birnin Landan.

Wani ɗan Najeriya yayi takakkiya zuwa Landan don kai ma Buhari sakon ‘Allah ya baka lafiya’

Wani ɗan Najeriya yayi takakkiya zuwa Landan don kai ma Buhari sakon ‘Allah ya baka lafiya’

Ajisafe wanda ya kai ziyara masaukin shugaba Buhari, wato gidan Abuja a birnin Landan ranar Alhamis 16 ga watan Feburairu, inda ya hada da wasu furanni duk ya mika ma shugaba Buharin.

KU KARANTA: Yadda aka tsige Muduru aka sauya shi da Kusada a matsayin kaakakin majalisa

Cikin sakon da Ajisafe ya aika ma Buhari, yayi mai fatan Allah ya tashi kafadarsa, ya bashi lafiya kuma Yayi masa jagora a harkar mulki.

Ga hotunan katin da furannin da Ajisafe ya kai ma Buhari:

Wani ɗan Najeriya yayi takakkiya zuwa Landan don kai ma Buhari sakon ‘Allah ya baka lafiya’
Wani ɗan Najeriya yayi takakkiya zuwa Landan don kai ma Buhari sakon ‘Allah ya baka lafiya’

Sakon nasa yace:

“Ya shugaban kasa Muhammadu Buhari, ina fatan addu’o’in da nake yi maka zasu kara maka kwarin gwiwa, da koshin lafiya,

Ya shugaba Buhari, ina fatan idan ka leko waje, zaka ga rana na haskawa, alamce na cewar Allah zai baka lafiya.

Jama’a da dama sun kosa ka dawo gida, don daidaitar da kasar. Ina fatan wannan kati da furanni dana kawo maka zasu tabbatar maka da yadda muke son ka. Ina fata Allah ya baka lafiya, yayi maka jagora kuma albarkace ka.

Nine naka, Akinjide Ajisafe.”

Muma a nan muna taya shugaba Buhari addu'an Allah ya bashi lafiya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel