YANZU-YANZU: Yan Boko Haram 7 sun mutu, mayakan sa kai 8 sun jikkata

YANZU-YANZU: Yan Boko Haram 7 sun mutu, mayakan sa kai 8 sun jikkata

Rahotannin dake iso mana yanzu yanzu suna nuni da cewa yan Boko Haram din da basu gaza 7 ba ne suka mutu yayin da mutane 8 cikin mayakan sa kai na civilain JTF suka jikkata a wasu hareren bama-baman da aka kai a garin Maiduguri cikin daran jiya Alhamis.

YANZU-YANZU: Yan Boko Haram 7 sun mutu, mayakan sa kai 8 sun jikkata

YANZU-YANZU: Yan Boko Haram 7 sun mutu, mayakan sa kai 8 sun jikkata

Hukumar agajin gaggawa ta jihar Borno ta bakin shugabanta Engr. Ahmed Satomi ne ya tabbatar wa da majiyar mu aukuwar hakan. Shugaban yace motocin su na daukar marasa lafiya kimanin 13 da suka je wurin da lamarin ya auku aka kone a unguwar garejin Muna.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta amince tayi karin albashi

Shugaban ya kara da cewa tabbasa jiya kam bada zo masu da kyau don kuwa yace mayakan Boko Haram din sun zo ne da niyyar su halaka su su kuma bata masu dukkan kayayyakin su da abincin da suke badawa na agaji.

A wani labarin kuma, Rundunar sojin saman Najeriya ta ce wasu 'yan Boko Haram sun kai wa wani jirginta mai saukar ungulu hari a lokacin da yake kai ma'aikatan lafiya garin Gwoza na Jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

A wata sanarwa da kakakinta, Guruf Kyaftin Ayodele Famuyiwa, ya sanya wa hannu, rundunar ta ce mayakan na Boko Haram sun yi harbe-harbe a kan jirgin kirar Mi-17, amma kuma ba wanda ya rasa ransa ko da yake matukin jirgin ya yi rauni.

Jirgin saman mai saukar ungulu dai ya tashi ne daga Maiduguri don kai ma'aikatan wadanda ke gudanar da wani shiri na kwanaki biyu na taimaka wa marasa lafiya a garin na Gwoza.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel