Musabbabin rikici tsakanin gwamna El-Rufa’i da Sanata Shehu Sani

Musabbabin rikici tsakanin gwamna El-Rufa’i da Sanata Shehu Sani

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana rashin amincewa ya nada yaran sanata Shehu Sani mukaman kwamishina ne ya janyo rikicin dake tsakaninsu wanda yaki ci yaki cinyewa.

Musabbabin rikici tsakanin gwamna El-Rufa’i da Sanata Shehu Sani

Musabbabin rikici tsakanin gwamna El-Rufa’i da Sanata Shehu Sani

El-Rufa’i ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da jaridar The Nation a Kaduna, inda yace yaki ya amincewa da sunayen wadanda Shehu Sani ya aiko mai dasu ne saboda rashin cancanta da karancin kwarewa, don haka ba zasu iya rike mukamin kwamishina ba, ba wai don ya kada dan takararsa ba a zabukan gwada kwanji na kujerar sanata ba.

Gwamnan yace a tunanin Shehu Sani, shine ya kitsa korar da aka yi masa daga jam’iyyar APC akan zargin ya ci mutuncin shugaba Buhari, gwamnan yace ba gaskiya bane, bashi da hannu a korar nasa. Sai dai gwamnan yace dama ai Shehu Sani nada muradin kujerar gwamna don haka bai yi mamakin adawar da yake yi da shi ba.

KU KARANTA: Gwamnati ta kammala tsatstsaran tsarin farfado da tattalin arzikin kasa

Gwamnan yace “babban abin dake damun Shehu Sanin a farko shine ban nada wani daga cikin mutanensa kwamishina ba. Amma a jihar kamar Kaduna, wanda take da sama da mutane 100,000 masu digiri har da digirgir, babu yadda za’a yi in nada mai difloma kwamishina kawai don Shehu Sani ne ya aiko da sunansa, ba haka nake ba.

“Gaskiya ne Shehu Sani yayi takaran cikin gida na sanata kuma ya kada wanda nake goyon baya a zabukan cikin gida (Sani Saleh), amma baya bina bashin komai, saboda sai dana bukaci kowannensu ya kawo min sunayen wanda yake ganin zasu iya zaman kwamishina, kuma sun aiko min, amma babu ko daya daga cikin mutanen Shehu Sani daya cancanci zama kwamishina.

“Toh saboda wannan ne fa yake ta zagi na tare da cin mutuncin Buhari, don haka ne ita kuma jam’iyya ta ladabtar da shi, amma duk da haka ya daura min hakki, a tunaninsa ni na sallame shi, amma maganan gaskiya itace, ko kadan bana ma tunanin Shehu Sani.

“Ina ganin, matsalar Shehu Sani itace, shi kwamared ne, do haka yake ganin indai yana son ya kai bantan sa a siyasa shine ya kasance ana jinsa koda yaushe a kafafen watsa labarai. Amma ina so in sanar da shi siyasa ba haka take ba. Sa’annan yana ganin hanyar da zai bi ya zama gwamna a Kaduna itace ya dinga sukar duk abinda na yi

“A gaskiya ban tunanin Shehu Sani barazana gare ni a siyasa ko kadan, idan aka buga gogen siyasa a 2018, zamu ga wanda jama’a ke so a Kaduna.”

A wani labarin kuma gwamnan ya dage ba zai nemi gafarar kowa ba don ya biya fulanin da aka kashe ma dabbobi diyya, inda yace hakan na daya daga cikin hanyar samun zaman lafiya a yankin kudancin Kaduna.

Sa’'annan ya kara da cewa shima tsohon gwamna marigayi Yakowa haka yayi a bayan bayan zabukan 2011.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel