Yan ta’addan Boko Haram sun kai hari garin Maiduguri, da dama sun mutu

Yan ta’addan Boko Haram sun kai hari garin Maiduguri, da dama sun mutu

An samu tashin hankali a kewayen birnin Maiduguri dake jihar Borno, lokacin da wasu yan ta’addan Boko Haram suka jefa manyan bama-bamai a yunkurinsu na kai hari wani sansanin yan gudun hijira.

A cewar wasu majiyoyi a kan Facebook dake zaune a birnin, an kai harin ne a daren ranar Alhamis, 16 ga watan Fabrairu lokacin da yan ta’addan sukayi kokarin mamaye sabon gidan Kwastam da aka gina inda aka sauke yan gudun hijira daga karamar hukumar Mafa.

Amma dai sun tarar da adawa yayinda sojoji suka far masu da musayar wuta wanda ya kai kimanin sa’a daya.

An rahoto cewa yan farar hula da dama wanda ba’a tabbatar da adadinsu ba sun rasa rayukansu yayinda aka kashe yan ta’addan harda wasu yan kunar bakin wake.

Yan ta’addan Boko Haram sun kai hari garin Maiduguri, da dama sun mutu

A cewar Zanna Yakub Lawan mutane da dama sun samu rauni a harin bazatan.

Ya rubuta: “Alhamdulillahi da na kasance a raye. Anyi nasara a kan harin. Yan Boko Haram sunyi kokarin kai hari birnin Maiduguri, amma dakarun sojin mu sunyi nasara a kansu.

Yan ta’addan Boko Haram sun kai hari garin Maiduguri, da dama sun mutu

“Sunyi kokari kai hari Yerwa ta sabon gidan Kwastam da aka gida inda yan gudun hijira ke zama daga Ajiri da Anadua a karamar hukumar MAFA (wani kyaftin a hukumar soji) ya bayyana cewa sojoji sun kashe dukkan yan Boko Haram din da kuma yan kunar bakin wake da dama wanda sukayi kokarin tayar da Yerwa.

“A halin yanzu, an rasa rayuka da dama sannan wasu da dama sunji raunuka. Ina buga wannan bayani ne, a yanzu haka muna kusa da gidanmu a 505 (Housing Units a nan Maiduguri); hukumomin tsaro da motocin asibiti sunyi layi dauke da wadanda abun ya shafa daga Muna-sansanin Kwastam zuwa asibiti.

Yan ta’addan Boko Haram sun kai hari garin Maiduguri, da dama sun mutu

“Allah yaji kan wadanda suka mutu sannan kuma Allah yaba wadanda sukaji rauni lafiya.”

A safiyar Juma’a, 17 ga watan Fabrairu, Maiduguri ya koma kwanciyar hankali bayan tashin hankalin da aka jiga a cewa waniu Mista Ayemigba wanda ke zama a yankin.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel