‘Yan Majalisun dokokin Jihar Legas sun bar PDP

‘Yan Majalisun dokokin Jihar Legas sun bar PDP

– ‘Yan Majalisun dokokin Jihar Legas da dama sun sauya sheka

– ‘Yan Majalisun sun bar PDP ne zuwa APC mai mulki

– PDP ta rage da ‘ya ‘ya biyu tak a Majalisar

‘Yan Majalisu 6 sun bar PDP zuwa APC

‘Yan Majalisu 6 sun bar PDP zuwa APC

‘Yan Majalisun dokoki na Jihar Legas da dama sun sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC mai mulki. Jam’iyyar APC dai ta kara samun karin rinjaye kenan a Majalisar Jihar.

‘Yan Majalisu 6 ne dai suka tsero daga PDP inda suka komo Jam’iyyar APC mai mulkin Jihar da ma kasar. Kilakin rikon kwarya na Majalisar Mista Aziz Sani ya karanto wasika inda ta ke nuna sauyin shekar ‘Yan Majalisun. ‘Yan Majalisun dai sun koka da irin rikicin da ya addabi PDP.

KU KARANTA: Yadda aka tsige Kakakin Majalisar Katsina

Honarabul Akeem Bello da Misis Mosunmola Sangodara suna cikin wadanda suka bar PDP. Sannan kuma akwai Jede Idimogu, Oluwa Fatai, Olusola Sokunle, da Dayo Famakinwa. Yanzu haka dai ‘Yan Majalisu biyu tak suka rage a PDP a Majalisar.

Haka dai kwanaki Wasu ‘Yan Majalisan dokokin Jihar Jigawa suka yi hannun riga da Jam’iyyar PDP su ka koma Jam’iyyar APC mai mulki. ‘Yan Majalisun sun ce Jam’iyyar PDP mai adawa ta zama ba ta da tsari.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel