Gwamnati za ta kashe kusan Miliyan 100 kan tayoyin mota

Gwamnati za ta kashe kusan Miliyan 100 kan tayoyin mota

– Gwamnatin Tarayya za ta kashe kudi Miliyan N94.5 wajen sayen tayoyin mota

– Wadannan tayoyi dai ba su jin harbin harsashi

– Haka nan kuma Gwamnatin Buhari za ta kashe kusan Miliyan N100 wajen abinci

Gwamnati za ta kashe kusan Miliyan 100 kan tayoyin mota

Gwamnati za ta kashe kusan Miliyan 100 kan tayoyin mota

Gwamnatin tarayya ta ware wasu makudan Miliyoyin kudi da za ta kashe domin sayen tayoyin motocin shugaban kasa da kuma sauran manyan kusoshin gwamnati a cikin kasafin kudin wannan shekarar.

An kiyasta abin da Gwamnatin za ta kashe a kan tayoyi a kan Naira Miliyan N94.5. Sakataren gidan Gwamnatin Arabi Jalal ya bayyana haka a gaban wani kwamiti na Majalisar Dattawa. An dai ware wannan kudi a bara sai dai ba a samu fitar da su ba daga cikin kasafin kudin shekarar.

KU KARANTA: Buhari yayi magana daga Landan

Irin wadannan tayoyi dai harbin harsashi ba zai iya masu rauni ba. Haka kuma Gwamnatin tarayyar za ta kashe sama da Naira Miliyan 100 wajen kayan cin abincin shugaban kasa da mataimakan sa, sai dai mafi yawanci kudin tun na bara ne da ba a biya ba.

A Amurka kuma Sabon shugaban kasar Donald Trump yace bai gaji komai ba sai kwamacala daga mulkin tsohon shugaba Barrack Obama. Yace ba magiya yake yi ba sai dai kurum don Jama’a su sani, yace zai shawo kan matsalolin kasar.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga wasu masu zanga-zangar sai Buhari nan a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel