An ja daga: Za a buga tsakanin Magu da Gwamnoni

An ja daga: Za a buga tsakanin Magu da Gwamnoni

– Hukumar EFCC tana binciken yadda Gwamnoni suka kashe wasu kudi da aka ba su

– Sai dai da alamu hakan zai kawo rikici babba tsakanin EFCC da Gwamnonin

– Har yanzu Ibrahim Magu bai ce komai ba

An ja daga: Za a buga tsakanin Magu da Gwamnoni

An ja daga: Za a buga tsakanin Magu da Gwamnoni

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya za ta sa kafar wando daya da Gwamnonin Najeriya. Kwanan nan ne dai Gwamnatin tarayya ta maidawa Jihohi wasu kudin bashi da aka biya, EFCC kuma ta sa ido ta ga inda aka kai kudin.

Gwamnonin kasar sun zauna ne a Fadar shugaban kasa a Birnin Tarayya Abuja inda ake tunanin suka fadawa shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu cewa shege-ka-fasa kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ce. An dai mikawa Gwamnonin Jihohin sama da Naira Biliyan 500.

KU KARANTA: Abin da ya sa muka hana Fayose kudi-Gwamnatin tarayya

Shugaban Gwamnonin kasar Abdul-Aziz Yari na Jihar Zamfara yace suna goyon bayan yaki da cin hancin wannan Gwamnati kuma za su jira Ibrahim Magu yayi binciken sa. Ba mamaki Gwamnonin na karkatar da wannan kudi ne wanda aka ce su biya bashin albashi.

Kwanki wani babban Kotun Tarayya da ke Garin Kano ya bada dama Gwamnatin tarayya ta rike makudan kudin da EFCC ta samu daga gidan Tsohon Manajan Kamfanin main a Najeriya watau NNPC Andrew Yakubu. Kwanan kuma wata Kotun ta bada irin wannan hukunci game da wasu Biliyan 30 da aka samu daga hannun Tsohuwar Minista Diezani Madukwe.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel