Mun yarda da shugaba Muhammadu Buhari – Inji Sarkin Ilorin

Mun yarda da shugaba Muhammadu Buhari – Inji Sarkin Ilorin

Mai martaba sarkin Ilorin, Dokta Ibrahim Sulu Gambari ya ce, sarakuna za su ci gaba da bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari goyon baya na ganin cewa gwamnatinsa ta ci nasara saboda shi mutum ne mai gaskiya.

Mun yarda da

Shugaba Muhammadu Buhari

Gambari ya bayyana wannan labari a lokacin da ministan labaru da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya kai masa ziyara a fadarsa a cikin wata tawaga da wasu ministoci 6.

Sarikin ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake jawabi a madadin sauran sarakuna. Ya ce za mu bayar da gudunmuwar mu a kowane lokaci kuma a ko'ina da gwamnati ta bukace mu.

Mun amince da shugaban wannan kasa, mun san shi mutun ne mai ladabi da biyaya ga al’umma kuma muna masa fatan alheri.

KU KARANTA KUMA: Za mu maida masallatai zuwa makarantu – Inji Sarkin Kano

Kuma sarkin ya nuna amincewa da 'yan majalisar ministoci na kasar, musamman wadanda suka kai ziyara a fadarsa . Ya ce kune wakilin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Muna mai imani cewa wannan gwamnati za ta yi tasiri a kan al'umma da kuma jama'a gaba daya.

Sarkin ya kira ‘yan Najeriya da babban murya da su ba gwamnati goyon baya cinma canji da ta yi alkawari.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel