Robert Mugabe ya caccaki Amurka

Robert Mugabe ya caccaki Amurka

- Shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe, ya bayyana ambasadan Amurka da ke kasar, Harry Thomas, da 'mugun iri' wanda ya kamata ya je ya 'rataye kansa a bishiyar Ayaba

- Mai magana da yawun shugaban, Geoerge Sharamba, ya bayyana hakan ne a wata jaridar gwamnatin kasar, mai suna 'Herald'

Robert Mugabe ya caccaki Amurka

Robert Mugabe ya caccaki Amurka

Wannan dai yana zuwa ne bayan da Ofishin jakadancin Amurka ya wallafa wata sanarwa ta shafin Twitter, a inda ofishin ya yi Allah-wadai da ci gaba da tsare Fasto Evan Mawarire da Fasto Patrick Mugadza.

Fastocin biyu dai sun yi hasashen cewa mista Mugabe zai mutu ranar 17 ga watan Oktoba.

Ana dai zargin Fasto Mawarire da yi wa kasa 'zagon-kasa', bayan ya dawo daga Amurka makon da ya gabata.

Shi kuma Fasto Mugadadza, an tsare shi ne ranar 16 ga Janairu, a inda kuma ake tuhumar sa da cin zarafin mutanen da yake da bambancin kabila da addini da su.

Tun dai 1987 Robert Mugabe yake mulkin Zimbabwe, al'amarin da ya janyo 'yar tsama tsakanin shugaban da Yammacin Turai musamman Amurka.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel