Barcelona ta kai wasan karshe na gasar Copa del Rey

Barcelona ta kai wasan karshe na gasar Copa del Rey

Luis Suarez ya zura kwallo koda yake an kore shi daga wasa a yayin da Barcelona ta kai zagayen karshe na cin kofin Copa del Rey da maki 10 a kan Atletico Madrid a Nou Camp.

Ita ma dai Madrid 'yan wasa goma ne suka buga mata wasan.

Barcelona ta kai wasan karshe na gasar Copa del Rey

Barcelona ta kai wasan karshe na gasar Copa del Rey

Suarez ya zura kwallon ne a minti na 43, gabanin a kori dan wasan Barcelona Sergi Roberto da takwaransa na Atletico Yannick Carrasco bayan an ba su katin gargadi guda biyu.

Kevin Gameiro ya zubar da bugun fenaretin da aka ba su, koda yake daga baya ya zura kwallon da ta sa suka yi kunnen-doki.

Daga nan ne aka bai wa Suarez katin gargadi a karo na biyu don haka ba zai buga wasan karshe ba.

Yanzu dai Barcelona za ta fafata da ko dai Alaves ko kuma Celta Vigo, wadanda za su yi karawarsu a ranar Laraba, a wasan karshe na cin kofin Copa del Rey.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel