Shugabannin APC 19 sun tabbatar da goyon bayan su ga Buhari

Shugabannin APC 19 sun tabbatar da goyon bayan su ga Buhari

Shugabannin jam'iyyar APC na jihohin arewa goma sha tara sunyi taron jaddada goyon bayansu ga Shugaba Muhammad Buhari a Abuja tare da yi masa godiya.

Shugaban APC na jihar Borno Alhaji Ali Bukar Dalori shi ya zanta da Muryar Amurka inda ya bayyana makasudin taron da abubuwan da suka cimma.

Shugabannin APC 19 sun tabbatar da goyon bayan su ga Buhari

Shugabannin APC 19 sun tabbatar da goyon bayan su ga Buhari

Inji Alhaji Dalori su shugabannin APC na arewa gaba daya sun yi taro sun ga kuma ya kamata su mikawa shugaban kasa Muhammad Buhari godiyarsu tare da nuna masa goyon bayansu. Sun yi farin ciki da abubuwan da yayi, fatansu kuma shi ne Allah ya barshi ya kuma cigaba da yin ayyukan alheri.

KU KARANTA KUMA: Wata mata ta maka mijinta kotu saboda fitsarin kwance

Shugaba Buhari ya taimakawa mutanensu inji Alhaji Dalori kuma ya kawo tsaro abun da babu da. Buhari ya dukufa da kwato hakkin jama'a daga wadanda suka wawuresu saboda haka jama'a su tashi su taimaka masa.

Akan batun rashin lafiyar shugaban, Alhaji Dalori yace hutu ne ya je saboda siyasa ce 'yan adawa suka shigo da ita akan lafiyar shugaban.

Dangane da wasu matsaloli da suke kunno kai kamar karancin man fetur a wasu wurare Alhaji Dalori yace wadanda suka yi barna da can suke haddasa lamarin domin cimma muradunsu.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel