‘Yan Najeriya 116 aka hallaka a kasar Afrika ta kudu cikin shekaru biyu – Gwamnatin tarayya

‘Yan Najeriya 116 aka hallaka a kasar Afrika ta kudu cikin shekaru biyu – Gwamnatin tarayya

- Gwamnatin tarayya ta bukaci gwamnatin kasar Afrika ta kudu tayi bincike da kuma gurfanar da wadanda suka hallaka yan Najeriya a Johannesburg a Disamban 2016

- Kana kuma tayi kira akan kisan Pretoria da zaluncin da ake wa mutane a kasar Afrika ta kudu

- Mai taimakon Buhari akan harkokin wajen Najeriya, Abike Dabiri-Erewa, tace kamata ayi Najeriya da kasar Afrika ta kudu su dinfa hadakan da zai kawo cigaban tattalin arzikin kasashen biyu

Kasar Afirka ta kudu tayi binciken kisan ‘yan Najeriya 116 kasar cikin shekaru biyu – Gwamnatin tarayya

Kasar Afirka ta kudu tayi binciken kisan ‘yan Najeriya 116 kasar cikin shekaru biyu – Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta bukacin gwamnatin kasar Afrika ta kudu ta gudanar da bincike kuma ta azabtar da wadanda ke da hannu cikin kisan yan Najeriya a Johannesburg a Disamban 2016.

Kana kuma tayi kira akan kisan Pretoria da zaluncin da ake wa mutane a kasar Afrika ta kudu.

KU KARANTA: Gwamna Al Makura ya sallami kwamshihanoni 9

Rahoton jaridar Punch tace Mai taimakon Buhari akan harkokin wajen Najeriya, Abike Dabiri-Erewa, wacce ta kai ziyarar ofishin jakadan kasar Afrika takudu, Lulu Mnguni, a Abuja a ranan Talata, 7 ga watan Febrairu ta bukaci tabbacin cewa za’a daina zaluncin da akeyiwa yan Najeriya a kasar Afrika ta kudu.

Ta kai wannan ziyara ne bayana an hallaka wani dan Najeriya, Tochukwu Nnadi, a watan Disamban 2016 wanda yan sanda sukayi.

Kana kuna Abike Dabiri-Erewa tayi korafi akan yan Najeriya 116 da aka kashe cikin shekaru 2 a kasar Afrika ta kudu. Tace yawancin kisan yan sanda kasar ne sukeyi.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

NAIJ.com
Mailfire view pixel