Fani-Kayode ya caccaki Lai Mohammed

Fani-Kayode ya caccaki Lai Mohammed

Tsohon ministan jirgin sama Femi Lai Mohammed ya caccaki ministan labarai da al’adu, Lai Mohammad kuma y ace masa maras lafiya.

Makaryacin banza, Ba kada lafiya; Fani-Kayode ya caccaki Lai Mohammed

Makaryacin banza, Ba kada lafiya; Fani-Kayode ya caccaki Lai Mohammed

A watan Magana da yayi a yau Laraba, 8 ga watan Febrairu ta shafin ra’ayi da sada zumuntarsa ta Tuwita, Fani Kayode ya soki Lai Mohammed akan maganarshi na cewa musulmai basu taba kashe kiristocin Najeriya a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ba.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta yi gaba da Shema

Yace : “ Makaryaci Lai Mohammed yayi ikirarin cewa shirme ne a ce musulmai sun kasa kirista a Najeriya. Wannan ya wuce makaryaci ma, bashi da lafiya."

Mutane da suna caccakan Lai Mohammed kwanakin nan akan karereayin da yakeyi na kuru-kuru.

Ministan ya musanta wadannan soke-soke da ake masa kuma ya kalubalanci masu yi masa cewa su kawo hujjansu.

A bangare guda, Fani Kayode ya yabawa mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo akan aiki sunan mukaddashin alkalin alkalai Jastis Walter Onnoghen zuwa majalisar dattawa domin tabbatar da shi.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel