Makiyaya sun shiga yajin aiki, sun daina kai shanu kasuwan jihar Oyo

Makiyaya sun shiga yajin aiki, sun daina kai shanu kasuwan jihar Oyo

Fulani makiyaya dake garin Ibarapa na jihar Oyo sun sha alwashin dakatar da kai shanunsu kasuwar dabbobi da aka fi sani da suna Kara dake garin Igbo Ora sakamakon kashe musu dabbobi da ake yi.

Makiyaya sun shiga yajin aiki, sun daina kai shanu kasuwan jihar Oyo

Shugaban kungiyar Fulani makiyaya Jamu Nati Fulbe, Abdulkadir Salihu ya shaida ma jaridar Daily Trust haka a jihar Legas, inda yace manoman yankin sun cigaba da kashe musu dabbobinsu duk da shiga tsakani da gwamnatin jihar ta yi.

Ita dai kasuwan Kara dake garin Igbo Ora ita ce babban kasuwar hada hadan dabbobi a gaba daya yankin Ibarapa da makwabtansa a jihar Oyo.

KU KARANTA: 'Zamu mayar da Sojoji gida ga iyalansu" - Buratai

Shugaban kungiyar Jamu Nati Fulbe, Abdulkadir Salihu yayi zargin ana amfani da guba ne wajen kashe dabbobin, inda ya nuna bacin ransa da zuwa yanzu babu wani takamaimen mataki da hukumomi suka dauka dan magance kashe kashen.

A cewarsa wannan ne ya sanya su dakatar da duk wani nau’in ciniki ko hada hadan dabbobi a kasuwar Igbo Ora, sa’annan zasu dauki matakin daya dace. Salihu yace suma kungiyoyin mahauta sun basu goyon baya, inda suka shiga yajin aikin suma.

Salihu yace “kimanin shanu hudu aka kashe mana a Igbo Ora a ranar Litinin, haka ma an kashe guda uku a garin Jigangan, a yanzu akwai wasu da dama da muke basu magunguna sakamakon cin guba da suka yi wanda aka basu.

“da ba dan na shiga maganar ba, da an gwamba tsakanin mutanen mu da yan garin, amma nayi kokarin shawo kan mutanen mu, kun san dai yadda matsayin shanu yake a wajen bafulatani, amma duk da haka ana ta cigaba da salwantar mana da arzikin mu.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana zaune kalau: Wani Dalibi ya aika abokin sa lahira cikin dare

Ana zaune kalau: Wani Dalibi ya aika abokin sa lahira cikin dare

Ana zaune kalau: Wani Dalibi ya aika abokin sa lahira cikin dare
NAIJ.com
Mailfire view pixel