Al-Makura ya sallami kwamishinoni 9, ya naɗa 9

Al-Makura ya sallami kwamishinoni 9, ya naɗa 9

Gwamnan jihar Nassarawa, Umaru Tanko Al-Makura ya fatattaki kwamishinoninsa guda 9 daga mukamansu, inda ya aika ma majalisar dokokin jihar sunayen wasu sabbin mutane guda 9 daya ke muradin nada su mukamin kwamishinoni don tantancewa.

Al-Makura ya sallami kwamishinoni 9, ya naɗa 9

Al-Makura a majalisar dokokin jihar Nassarawa

Kaakakin majalisar dokokin jihar Nassarawa Ibrahim Balarabe Abdullahi ya karanta wasikar da gwamnan ya turo ma majalisar, bayan shugaban masu rinjaye Tanko Tunga ya gabatar da sunayen da gwamnan ya aiko musu.

KU KARANTA: Kungiyoyin kwadago zasu gudanar zanga zanga a ranar alhamis

A ranar Litinin 6 ga watan Feburairu ne gwamnan ya sallami wasu daga cikin kwamishinoninsa, inda ya canza ma guda biyu ma’aikata, sa’annan ya kyale guda hudu a ma’aikatunsu.

Al-Makura ya sallami kwamishinoni 9, ya naɗa 9

Dan majalisa Tanko Tunga yace, “ya ku abokan aikina, ga sako daga mai girma gwamna Tanko Al-Makura yana neman mu tantance tare da tabbatar da sunayen wasu mutane 9 daya ke son nadawa mukamin kwamishinoni.”

Mutanen da aka turo da sunayensu sun hada da Prof.Jonathan Yakubu daga karamar hukumar Akwanga, Mary Enwongulu daga Nassarawa Eggon, Alhaji Mohammed Jamil Zakari daga Awe, Bamaiyi Anangba daga Kokona, Tanko Zubairu daga karamar hukumar Doma, Engr Wada Yahaya daga Keffi, Dr. Abdulkarim Kana daga Kokona, Ayuba Ayinaje daga Toto, sai Hon Abdulhamid Kwara daga Wamba local government area.

Kaakakin majalisar dokokin Balarabe Abdullahi ya umarci wadanda aka turo da sunayen nasu dasu gurfana gaban majalisar a ranakun 13 zuwa 15 ga watan Feburairu don tantancewa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel