Babban Lauya ya soki shugaba Buhari game da rashin lafiyar sa

Babban Lauya ya soki shugaba Buhari game da rashin lafiyar sa

– Babban Lauyan kasa Femi Falana ya soki Shugaban kasa Muhammadu Buhari

– Femi Falana yace bai dace shugaban ya rika boye rashin lafiyar sa ba

– Falana yace ya dace ‘Yan Najeriya su san halin da shugaban kasa yake ciki

Babban Lauya ya soki shugaba Buhari game da rashin lafiyar sa

Babban Lauya ya soki shugaba Buhari game da rashin lafiyar sa

Babban Lauyan nan na kasa Femi Falana SAN ya soki shugaba Muhammadu Buhari game da al’amarin rashin lafiyar sa. Falana yace ya kamata ace ‘Yan Najeriya sun san halin da shugaban su yake ciki.

A wata hira da Falana yayi da Gidan Talabijin na Channels yace muddin mutum ya shigo harkar siyasa to kuma babu maganar sirri ko nuku-nuku musamman a ce shugaban kasa baki daya. Falana yace ya kamata ayi wa dokokin kasar garambawul domin a san yadda shugaban kasa yake ciki.

KU KARANTA: Mai magana da bakin Buhari yace ya dade bai ji ta bakin sa ba

Falana yace a bara shugaban kasar ya bayyana abin da ya kai sa kasar waje, haka wannan karo ya kamata yayi wa ‘yan kasa bayani. Hakan dais hi zai rage yada rade-radi dabam dabam a cikin Kasar.

A jiya ne Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kara tabbatar da cewa Muhammadu Buhari na nan cikin koshin lafiya. Osinbajo yace kuma Buhari zai dawo Najeriya yana kammala gwajin da yake yi a asibiti.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel