Lai Mohammed: Mu ba masu neman fitina bane-CAN

Lai Mohammed: Mu ba masu neman fitina bane-CAN

– Kungiyar CAN ta soki Minista yada labarai na kasa

– CAN ta ce karya Lai Mohammed yake yi game da maganar da yayi

– Lai Mohammed ya zargi shugabannin addinai da kokarin tada rikici

Lai Mohammed: Mu ba masu neman fitina bane-CAN

Lai Mohammed: Mu ba masu neman fitina bane-CAN

Kungiyar CAN ta Kiristocin Najeriya ta yi ca a kan Ministan yada labarai na Najeriya Alhaji Lai Mohammed. CAN ta zargi Minista Lai Mohammed da kokarin birne abubuwan da ke faruwa a kasa ga Kiristoci.

Shugaban Kungiyar CAN din Dr. Samson Ayokunle yace ba su ji dadin kalaman Lai Mohammed ba, ko da yake ba su yi mamakin haka ba. Lai Mohammed ya zargi shugabannin Addinai da kokarin tada rikici a kasa shekaran jiya da gwamnatin tarayya tayi taro Garin Ilorin.

KU KARANTA: Yan Shi'a sun yi Bikin Kirismeti

Kungiyar CAN tace Ministan na kokarin boye abin da ke faruwa ga ‘Ya ‘Yan ta Kiristoci ne a kasar, amma su ba masu tada hankali bane. Har wa yau dai Kungiyar CAN din tana nema a sa kasar a addu’a. Kwanakin baya dai DSS ta kama wani Fasto da kokarin kawo hatsaniya.

Mai magana da bakin shugaban kasa Femi Adesina yayi karin haske game da rashin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke Landan yace kuma shugaba Buhari zai dawo kafin lokacin da ake tunanin. A baya Jaridar Sahara Reporters ta rahoto cewa Buhari na iya kara watanni hudu a Landan.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel