Ba sauki: EFCC ta kara kama tsohon Gwamna Shema

Ba sauki: EFCC ta kara kama tsohon Gwamna Shema

– Hukumar EFCC ta dai rutsa tsohon Gwamnan Katsina Barista Shema

– Da alamu EFCC ta kara damke Shema da wani sabon laifi kafin ya bar Kotu

– Ana binciken tsohon Gwamnan da laifin satan dukiyar al’umma

Ba sauki: EFCC ta kara kama tsohon Gwamna Shema

Ba sauki: EFCC ta kara kama tsohon Gwamna Shema

Tsohon Gwamnan Jihar Katsina Barista Ibrahim Shema dai ya ga ta kan sa. Don kuwa da alamu Hukumar EFCC ta kara damke sa bayan an tashi daga wata shari’a da aka yi da shi a kotu kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Yayin da ake shirin barin kotun, Jami’an Hukumar EFCC suka dura motar tsohon Gwamnan suke nemi ya biyo su, su ka kuma tuka motar sa a baya. Jaridar Daily Trust ce dai ta kawo duk abin da ya faru. Mai magana da yawun tsohon Gwamnan dai yace ba kama sa aka yi ba, Yanzu dai haka an daga karar.

KU KARANTA: Duba yadda ake barna da kudi

Dama can Hukumar EFCC ta nemi a kama tsohon Gwamnan a rufe a gidan yari, hakan zai sa ba za a neme sa a rasa ba a ko da yaushe. Jami’an ‘Yan Sanda dai sun kora Jama’a da ke kokarin zagaye kotun.

Tun kwanaki dai aka gurfanar da Tsohon Gwamnan na Jihar Katsina Barista Ibrahim Shehu Shema a gaban Babban Kotun Jihar da ke cikin Garin Katsina. Shema ya zargi Gwamnatin APC da makarkashiya, sai dai Gwamna Masari yace Shema ya ji da kan sa.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel