Zamu daina shigo da tacaccaen mai daga 2019 - Ibe Kachikwu

Zamu daina shigo da tacaccaen mai daga 2019 - Ibe Kachikwu

- Najeriya zata daina shigo da tacaccen man fetur daga shekarar 2019 inji ministan man fetur

- Mr Ibe Kachikwu yace cikin shekara 2 masu zuwa, gwamnatin tarayya ta samu cigaba a ma’aikatan man fetur

Zamu daina shigo da tacaccaen mai daga 2019 - Ibe Kachikwu

Zamu daina shigo da tacaccaen mai daga 2019 - Ibe Kachikwu

Mr Ibe Kachikwu, ministan man fetur yace a ranan Talata,7 ga watan Febrairu cewa Najeriya zata daina shigo da man fetur daga shekarar 2019, a Abuja.

Yayinda yake Magana a wata taron duban kudin man fetur da majalisar wakilan tarayya ta shirya, Mr Kachikwu yace cikin shekaru 2, gwamnatin tarayya ta samu nasarar farfado da matatun man fetur din da suka durkushe a da.

KU KARANTA: An bamu kudi N200 - Amina yar Boko Haram

Wannan cigaba ya taimaka wajen samar da lita miliyan 8 cikin lita miliyan 20 da ake amfani da shi kowani rana a kasar.

Mr Ibe Kachikwu yayi bayanin cewa gwamnatin tarayya ta samar da wata mafita wanda zai birge masu sanya hannun jari domin hada kai da kamfanin NNPC domin gyara matatun man fetur cikin shekaru 2.

Yace: “ Wannan abu ya kasance manufar wannan gwamnatin saboda a watan Disamban 2018, NNPC zata cika aikin da aka bata , wanda yake shine a daina shigo da man fetur da kashi 60 cikin 100.

“Zuwa 2019, ya kamata mu daina shigo da man fetur gaba daya a wannan kasa. Kari da cewa Dangote na gina sabuwar matata, muna sa ran ma ma zai yi yawa.!

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel