Mun kwashe kwanaki 3 kan babur kafin muka shigo Maiduguri- Amina

Mun kwashe kwanaki 3 kan babur kafin muka shigo Maiduguri- Amina

Wata sabuwar harin Bam da aka kai babban birnin jihar Borno, Maiduguri a yau wanda wani ma’aikacin hukumar tsaro ta farin kaya wato Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) ya kawar.

Mun kwashe kwanaki 3 kan babur kafin muka shigo Maiduguri– Yarinyar da aka kama a Maiduguri da safiyar yau

Mun kwashe kwanaki 3 kan babur kafin muka shigo Maiduguri– Yarinyar da aka kama a Maiduguri da safiyar yau

Jaridar News Agency of Nigeria (NAN) ta bada rahoton cewa hukumar NSCDC a yau Talata, 7 ga watan Febrairu ta kawar wani harin Bam guda biyu wanda wasu yan kuna bakin wake sukayi niyyar kaiwa yayin suke kokarin shiga cikin yan babur a gidan man NNPC Mega Station Damboa, Maiduguri.

Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa yarinyar ta bayyana cewa yan Boko Haram din sun fada mata cewa zata shiga Aljannah idan ta tayar da Bam din.

KU KARANTA: Yarinyar da ta kai harin Bam da safen nan

Sun bamu N200 domin mu saya ma kanmu abinci. Sai da mukayi kwanaki 3 kan babur zuwa Maiduguri. An bamu umurnin cewa mu tayar da Bam din duk inda muka ga taron mutane.

Sunce idan muka danna abin, Bam din zai tashi, sai na fada musu ba zan iya tayar da Bm ba. Sai suka ce idan Zainab ta tayar da nata, babu matsala.

“Yayinda muke hanyar shiga Maiduguri, mun hadu da Soji kuma suna ta harbi. Abin ya bani tsoro kuma mutanen da suka kawomu suka arce.

“Ni yar bangaren Shekau ne, duk da cewa ban taba ganinshi ba, ina ji ana maganarshi a Gobarawa.”

Amina ta tace mahaifinta da mahaifiyarta da kaninta,Umar, sun hallaka ne yayinda suke kokarin tserewa daga wurin Boko Haram.

“Munzo daga Gobarawa ta hanyar Damboa, Madagalii da Algarno, wannan wuri ne da yawanmu anyi garkuwa da mu kuma an aurarwa yan Boko Haram.”

Kwamandan NSCDC, Abdullahi Ibrahim, yace an mika Amina ga kwamandan sojin 7 Division na Maiduguri domin zurfafa bincike.

https://web.facebook.com/pg/naijcomhausa/posts/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel