Za mu maida masallatai zuwa makarantu – Inji Sarkin Kano

Za mu maida masallatai zuwa makarantu – Inji Sarkin Kano

Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya shawarci gwamnonin arewa gaba daya da su fara mayar da masallatai zuwa makarantun firamare, musamman a kauyuka.

Za mu maida masallatai zuwa makarantu – Inji Sarkin Kano

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa mai martaba sarkin Kano ya furta wannan labari ne a lokacin wata gangamin shirin harkokin ilmi ta jihar Kano. Y ace: “Na kasance a Morocco wani lokaci da suka wuce da kuma na nema ganin jami'o'in su inda suka kai ni wasu masallatai inda na ga kowane masallaci na matsayin ajujuwan koyar da kimiyyan na’urar kwamfuta da sauran batutuwa. “

A cewar Sarkin Sanusi, masallaci ba wurin yin salla kadai ba ne, amma kuma za iya amfani da ita a matsayin wuri daura aure, koyar da ilimi da kuma horon ayyukan jagoranci.

Ya bayar da hujjar cewa ta yin amfani da masallatai domin wadannan ayyuka za su taimaka wajen rage yawan kashe-kashen kudi yayin da ya kara da cewa, idan har aka soma wannan ra'ayin, kudadin da aka ware saboda gine-ginen makarantu za a iya amfani da su wurin horon malamai.

KU KARANTA KUMA: Matashi dan shekara 20 ya lakada ma jami’in LASTMA dukan tsiya

A cikin jawabinsa, Gwamna Abdullahi Ganduje ta jihar Kano ya bayyana cewa, gwamnati ta kasha kudi naira biliyan 30 ga biyan albashin malamai koyarwa da kuma sauran ma'aikatan makarantu a duk karamar hukuma 44 ta jihar Kano.

Ya kara da cewa, ana fatan sa a zama da kwararrun malaman makaranta 25,000 a jihar Kano a wata sabon yunƙuri a shekara ta gaba.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel