‘Yan Majalisar Najeriya sun maka Gwamnatin Amurka a Kotu

‘Yan Majalisar Najeriya sun maka Gwamnatin Amurka a Kotu

– ‘Yan Majalisar Najeriya sun maka Gwamnatin Kasar Amurka a Kotu

– ‘Yan Majalisar na zargin Jakadan Kasar Amurka da bata masu suna

– Ana neman Gwamnatin Amurka ta biya ‘Yan Majalisun Dala Biliyan $1

‘Yan Majalisar Najeriya sun maka Gwamnatin Amurka a Kotu

‘Yan Majalisar Najeriya sun maka Gwamnatin Amurka a Kotu

‘Yan Majalisun Najeriya suna karar Gwamnatin kasar Amurka a Kotu inda su ke neman gwamnatin kasar ta biya su kudi har dala biliyan $1. ‘Yan Majalisun sun ce Jakadan Amurka yayi masu sharrin lalata da ‘yan mata.

Wadannan ‘Yan Majalisu guda 3; Hon. Terse Mark, Samuel Ikon da Muhammadu Gololo suna zargin Gwamnatin Amurka da yi masu sharrin cewa sun yi lalata da mata da karfi da ya ji a shekarar bara a Amurka, wanda kazafi ne aka yi masu.

KU KARANTA: Yan Sanda sun yi wawan kamu; ta ritsa da Gwamna

Sai dai bayan an gudanar da bincike an gano cewa sharri ne kurum aka yi wa ‘Yan Majalisun na Najeriya. Tuni dai har ‘Yan Majalisun sun dauki hayar Lauya domin shari’a, dama can an haramtawa ‘Yan Majalisun shiga Kasar ta Amurka kwata-kwata.

Haka kuma Sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal zai bayyana a gaban Sanatocin Najeriya inda zai kare kasafin kudin bana na Ofishin sa wanda ya kusa kai Naira Biliyan 10. Kasafin kudin bana na Ofishin ya kara yawa da sama da Naira Biliyan 2.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel