Masu ciwon Sikila su dubu 17 ne a jihar Katsina

Masu ciwon Sikila su dubu 17 ne a jihar Katsina

Wani rahoto na jaridar Daily Trust ya bayyana cewar jihar Katsina ce kan gaba a yawan masu dauke da ciwon Sikilia, inda take da kimanin mutane 17,000 masu ciwon, kamar yadda alkalumma daga ma’aikatar lafiya ta jihar suka nuna.

Masu ciwon Sikila su dubu 17 ne a jihar Katsina

Kwamishiniyar kiwon lafiya a jihar Katsina

Yayin dayake jawabi a bikin kaddamar da shirin tantance masu dauke da zazzabin cizon sauro da masu ciwon sikilia da gwamnatin jihar ta dauki nauyi tare da hadin gwiwar shirin uwargidar shugaban kasa Aisha Buhari na ‘Future Assured’, sakataren gwamnatin jihar Alhaji Mustapha Inuwa yace ciwon Sikila na matukar illata masu dauke da ita, ta yadda sama da kashi 50 cikinsu ke mutuwa a shekaru goma na farkon rayuwansu.

KU KARANTA: Jami’an tsaro na farin kaya sun daƙile harin kunar bakin wake a Maiduguri

Don nuna damuwarta da kalubalen da masu dauke da ciwon suke fuskanta ne gwamnatin jihar ta gina asibitoci na musamman a kananan hukumomin Katsina, Funtua, Malumfashi, Dutsin-ma, Daura da Ingawa don kulawa da marasa lafiyan.

A nata jawabin, kwamishiniyar kiwon lafiya a jihar, Hajiya Mariyatu Bala Usman tace an shirya tantancewar ne don wayar da kawunan dalibai da iyaye akan muhimmancin gwajin karfin jinin masoya kafin suyi aure, don haka ne ma gwamnati ta fara daga kan dalibai saboda ta haka ne za’a magance gadar da ciwon ga yaran da aka haifa.

Ana sa ran tantance dalibai mata sama da 1,250 a makarantun sakandari dake cikin garin Katsina.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

NAIJ.com
Mailfire view pixel