Kungiyoyin kwadago zasu gudanar zanga zanga a ranar alhamis

Kungiyoyin kwadago zasu gudanar zanga zanga a ranar alhamis

Gamayyar kungiyar kwadago wato NLC, da TUC sun yanke shawarar gudanar da gangamin zanga zanga don nuna bacin rai da halin matsin da ake ciki a kasar nan.

Kungiyoyin kwadago zasu gudanar zanga zanga a ranar alhamis

Zanga zangar da suka yi lakabi da suna ‘ranar nuna bacin rai ga cin hanci da rashawa tare da shugabanci mara kyau’ zai gudana ne a biranen Legas da Abuja.

KU KARANTA: Jami’an tsaro na farin kaya sun daƙile harin kunar bakin wake a Maiduguri

A jiya Litinin, shugaba kungiyar ma’aikata, NLC, Ayuba Wabba yayi ma yan jaridu jawabi dangane da shirin zanga zangar, inda yace zasu yi tattaki har zuwa fadar shugaban kasa da kuma majalisa, kuma zasu mika jerin bukatunsu ga fadar ta shugaban kasa da kuma majalisun dokokin kasar nan.

Wabba yace yayan kungiyarsu zasu fara taruwa da misalin karfe 7 na safiyar alhamis a filin Unity Fountain dake Abuja, daga nan kuma zasu rankaya zuwa sakatariyan ma’aikatan gwamnatin tarayya, sai su wuce majalisun dokokin kasar nan, inda kuma zasu karkare tattakin nasu a fadar shugaban kasa.

Wabba yace ya zama wajibi su gudanar da wannan gangami don nuna bacin ransu da karayar tattalin arziki, musamman tashin goron zabi da dalar Amurka keyi a kullum, sa’annan suna bakatar shuwagabannin su sauya salon mulkin da suke yi.

Wabba ya kara da cewa suna da bukatu da suka hada da karin karancin albashi, tare da magance matsalar rashin biyan albashi, daga nan ya cigaba da fadin za’a cigaba da gudanar da kwatankwacin wannan zanga zangar a kafatanin jihohin kasar nan.

Daga karshe yace dolen su ne a matsayinsu na shuwagabannin kungiyoyin kwadago da su jagoranci wannan gangami, kuma yace babu inda aka bukaci dan Najeriya ya nemi izinin yansanda kafin ya gudanar da zanga zanga.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon zanga zanga NLC a baya:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara: INEC ta kaɗa gangan siyasar 2019, ta sanya ranakun gudanar da zaɓen fidda yan takara

An fara: INEC ta kaɗa gangan siyasar 2019, ta sanya ranakun gudanar da zaɓen fidda yan takara

An fara: INEC ta kaɗa gangan siyasar 2019, ta sanya ranakun gudanar da zaɓen fidda yan takara
NAIJ.com
Mailfire view pixel