Yarintar da ta kai harin Bam Maiduguri da safen nan

Yarintar da ta kai harin Bam Maiduguri da safen nan

Wata sabuwar harin Bam da aka kai babban birnin jihar Boeno, Maiduguri a yau wanda wani ma’aikacin hukumar tsaro ta farin kaya wato Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC) ya kawar.

Yarintar da ta kai harin Bam Maiduguri da safen nan

Yarintar da ta kai harin Bam Maiduguri da safen nan

Jaridar News Agency of Nigeria (NAN) ta bada rahoton cewa hukumar NSCDC a yau Talata, 7 ga watan Febrairu ta kawar wani harin Bam guda biyu wanda wasu yan kuna bakin wake sukayi niyyar kaiwa yayin suke kokarin shiga cikin yan babur a gidan man NNPC Mega Station Damboa, Maiduguri.

KU KARANTA: Ku cire Buhari yanzu- wasu mtane

Kwamandan hukumar, Ibrahim Abdullahi, da ke Maiduguri yace wannan abu ya faru ne misalinkarfe 6:45 na safe.

“Ma’aikatanmu da ke aiki a gidan man NNPC sun damke yan mata biyu yan kunar bakin wake wadanda ke kokarin ciki layin masu sayan mai a gidan man NNPC misalin karfe 6.45 na safe.

“Daya daga cikinsu taji tsoro ta yar da Bam din kuma aka damke ta da wuri, dayar kuma ta fara gudu da Bam din, amma daya daga cikin ma’ aikatanmu ya harbeta a kafa.”

“Mun tura jami’an kawar da Bam wurin yanzu” Abdullahi yace

Saboda haka yana kira mutanen jihar Borno su kasance cikin afarga saboda yan kungiar Boko Haram na neman wuraren da akwai jama’a ne su tayar da tarzoma.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel