Karuwa ta cire hancin kanwarta a lokacin fada kan saurayi

Karuwa ta cire hancin kanwarta a lokacin fada kan saurayi

Hukumar yan sandan Najeriya ta kama wata karuwa mai suna Ebere Ugwu, kan zargin cire ma kanwarta hanci ta hanyar cizo a lokacin wani mumunnan rikici da ya shiga tsakaninsu.

A cewar wani rahoto daga PM Express, al’amarin mai ban al’ajabi ya faru ne a wani gurin shakatawa dake unguwar Church Street, Jakande a yankin Isolo dake jihar Lagas inda yan matan guda biyu ke rubibin neman abokanan hulda da suka zo daukarsu.

Karuwa ta cire hancin kanwarta a lokacin fada kan saurayi

An rahoto cewa Ifeoma, ta kawo kanwarta Lagas daga garinsu Abakaliki, jihar Ebonyi domin ta dunga ba abokanan cinikinta a gurin shan giya kyauta. Abun yazo ya zamana cewa Ifeoma, wacce ta kasance sabuwa kuma tafi yayarta kyau tafara jan hankulan samarin Ebere har ta kai Ebere bata da samari masu daukarta kuma.

KU KARANTA KUMA: Shugaban makaranta ya yi wa dalibi mugun duka saboda yayi fashi (hotuna)

A ranar da al’amarin zai faru, an bayyana cewa kamar kullun, wani abokin huldan Ebere ya barta ya kuma koma gurin Ifeoma. Ebere tace ta nemi kanwarta ta bar mata saurayin amma taki sai da ta kwana da shi. Bayan saurayin ya tafi, Ebere ta nemi kanwarta da ta bata naira dubu goma N10,000 wato kudin da saurayin nata ya saba biyan ta.

Wannan ne ya kai ga musayar kalamai tsakanin yan’uwan biyu wanda daga baya fada ya kaure a tsakaninsu a wannan hali ne, Ebere ta ciji Ifeoma a kan hancin ta.

An kai rahoton al’amarin ga hukumar yan sandan Ejigbo an kuma kama Ebere sannan an mika ta babban kotun Ejigbo, inda aka gurfanar da ita, ta kuma ki yarda da laifin ta.

Babban alkalin kotun, Akeem Fashola ya bayar da belin Ebere kan naira dubu hamsin (N50,000) da wasu ka’idoji biyu, koda dai tana karke a kurkuku zuwa lokacin da zata cike ka’idojin belin nata.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel