Obasanjo wani halitta ne tsakanin mutane – Inji tsohon gwamna

Obasanjo wani halitta ne tsakanin mutane – Inji tsohon gwamna

Tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo kwanan nan ya ce zai yi wa kasar Nijeriya kyau idon an samu shugaban kasa daga kabila Igbo.

Obasanjo

Tsohon gwamnan Jihar Anambra, Dr Chukwuemeka Ezeife, ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo wani halitta ne daban a tsakanin mutane.

Ezeife ya furta wannan a cikin wata hira da ya yi da jaridar The Punch bisa gazabenkasamaizuwa a shekarar 2019.

Dalilin da yasa na ce aka shine: A lokacin da Obasanjo yake rufe a kurkuku, mutane da yawa suna shirin yin takara shugaban kasa har da kaina a wannan lokacin.

Watarana, matata, Ugoeze, ta shawarceni cewa kar inbata kudina a kanneman shugabancin kasa saboda bakin alkalami ya riga ya bushe.

Na tambaye ta me nufin ta? Ta ce: “Obasanjo ne zai zama sabon shugaban kasa.”

Na ce Obasanjo na kurkuku. Amma ta sake jaddada cewa ta gani tsohon shugaban kasa Abdulsalami Abubakar na mika wa shugaba Obasanjo mulki a matsayin shugaban kasa kuma akarshe aka din ta faru. Za a iya tuna cewa, tundaga wannan lokacin shugaba Obasanjo yana da hannu da duk shugabanci da suka biyo bayansa.

KU KARANTA KUMA: Za mu maida masallatai zuwa makarantu – Inji Sarkin Kano

Ganin Obasanjo ya nuna sha’awar cewa ya kamata kabila Igbo suyi shugabancin kasar nan, Ezeife ya ce: “ Shine ya yi ruwa kuma ya yi saki ganin cewa tsohon shugaban kasa Jonathan ya kai ga karagar mulki bayan rasuwa tsohon shugaban kasa Yar’Adua.

Ko da shugaba Buhari amma, Obasanjo ya yi rawar ganin cewa Buhari ya ci nasara. Saboda haka, maganan Obasanjo ta na muhimmanci da gaskiye.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha

Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
NAIJ.com
Mailfire view pixel