Maganganu 3 tattare da rashin dawowan shugaba Buhari

Maganganu 3 tattare da rashin dawowan shugaba Buhari

A ranan Lahadi, 5 ga watan Febrairu, 2016, mutan Najeriya na cikin zaman zaton dawowan shugaba Muhammadu Buhari daga hutun da yaje kasan Landan tun watan Junairu kawai sai aka samu sanarwa daga bakin mai Magana da yawun shugaban kasa, Mr. Femi Adesina, inda yace shugaba Muhammadu Buhari ba sai samu daman dawowa ba saboda wasu dalilai da suka shafi lafiyarsa.

Maganganu 3 tattare da rashin dawowan shugaba Buhari

Maganganu 3 tattare da rashin dawowan shugaba Buhari

Jaridar NAIJ.com ta kawo muku abubuwa 3 tattare da rashin dawowan shugaba Buhari, ku sha karatu:

1. Shin da gaske bashi da lafiya ne?

Tambayar da yan Najeriya key i shine wai shin shugaba Buhari bashi da lafiya ne. ana cikin wannan zato shine a jiya, 7 ga watan Febrairu, mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya fasa kwai inda yace shi fa yayi Magana ta wayar sadarwa da shugaba Buhari kuma yana nan cikin koshin lafiya.

KU KARANTA: An kwato kudin magudin zabe N100m

2. Idan lafiyanshi kalau, shin me yasa ya daga dawowarsa?

Mutane kuma suna cewa shin idan yana cikin koshin lafiya mai yasa ya dakatar da dawowarsa ranan Lahadi? Ko kuma me yasa ba zai fito yayi Magana ga yan Najeriya ba domin a tabbatar da cewa lallai fa yana nan cikin rai da koshin lafiya.

3. Fadar shugabankasa kawai karya da yaudaran mutane sukeyi

Wasu bangaren mutane kuma yana tunani cewa fadar shugaban kasa kawai yaudaran mutanen Najeriya sukeyi saboda sunki bayyana ainihin abinda da ke daun shugaba Muhammadu Buhari, wana ya kai wasu na cewa ma ai yayi wafati.

A cikin wadannan batu guda 3, shin kai wane kafi gamsuwa da shi? Ku bayyana ra’ayoyinku.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017

Gwamnati ta karrama wadanda suka bada gudummawa wajen habakar kasuwanci a 2016/2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel