Abu 4 da yan Najeriya ke cewa tun bayan kin dawowar swhugaba Buhari

Abu 4 da yan Najeriya ke cewa tun bayan kin dawowar swhugaba Buhari

- Rashin dawowar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bayan shafe makwanni biyu yana hutu a London ya janyo cece-kuce tsakanin ‘yan kasar kan batun rashin lafiyarsa

- Wasu ‘Yan kasar na ganin tsawaita hutun shugaban ya tabbatar da ba ya cikin koshin lafiya, yayin da wasu suka karbi sanarwar da kakakinsa ya fitar da ke cewa shugaban na jiran sakamakon gwaje gwajen likitoci

Abu 4 da yan Najeriya ke cewa tun bayan kin dawowar swhugaba Buhari

Abu 4 da yan Najeriya ke cewa tun bayan kin dawowar swhugaba Buhari

A jiya Litinin ne dai ya kamata shugaban ya dawo kan aiki, amma a jiya lahadi Ofishinsa ya fitar da sanarwar tsawaita hutun bisa umurnin likitan da ke kula da lafiyarsa a London.

Sanarwar dai ta janyo cece-kuce kan lafiyar shugaban musamman rashin fadin lokacin dawowarsa da kuma bayani akan rashin lafiyar.

(1) Wasu na ganin shugaban ya dace ya fito a sakon bidiyo kamar yadda ya aikawa mutanen Bauchi da sanarwar soke zuwansa a jihar saboda hazo.

(2) Jam'iyyun adawa sun bukaci cikakken bayani akan rashin lafiyar shugaban bayan a can baya an ta yada jita-jitar cewa ya rasu.

(3) Buhari Network Group ta ce ya kamata masu nuna kin jinin gwamnatinsa su san cewa babu wata kasa da za ta cigaba ba tare da fuskantar matsin tatttalin arziki irin wanda Najeriya ke fuskanta yanzu ba.

(4) Shi kuwa Aliyu Tilde cewa yayi Allah ya bai wa Shugaban Kasa koshin lafiya, ya yafe masa kurakuransa da Zunubbanshi, ya shirye shi wajen shugabantar lamurranmu.

Shugaba a ko’ina abinda ya cancanta shi ne fada masa gaskiya a inda ake ganin ya yi kure; addu’ar shiriyar Ubangiji wajen shugabanci, da koshin lafiya da gafarar Allah.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998

Abubuwan da Abacha yaso yi washe-garin ranar da ya rasu a 1998
NAIJ.com
Mailfire view pixel