Abubuwa 3 da yasa Buhari ya dagar da dawowarsa

Abubuwa 3 da yasa Buhari ya dagar da dawowarsa

Akwai yawar jita-jita a yanzu wanda a ke zargin mutuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari. Sugaban kasan ya fara wata dogon hutu na kwana 10 wanda ya kamata ya dawo ranar Litini, 6 ga watan Fabrairu.

Abubuwa 3 da yasa Buhari ya dagar da dawowarsa

Shugaba Buhari

Duk da haka, shugaban kasa ya kara tsahon hutunsa zuwa wani lokaci nan gaba wanda ya kawo kace nace a tsakanin al’umma.

A bayan shugaba Muhammadu Buhari, an gudanar da ayyuka daban-daban wanda mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya jagoranta.

Za ku iya tuna cewa shugaban kasa ya bar kasar ne a ranar da ya sanarwar da shugaban majalisar dattijai. Wannan na nuna cewa shugaban ya fara hutun ne da wuri kafin ranar da ya sanya a cikin wasikan da ya rubuta wa ‘yan majalisar.

Wannan shine karo na uku da shugaban kasa zai je hutu tun da ya zama shugaban kasar tarayyar Nigeria.

KU KARANTA KUMA: Likitocin Asibitin Jami’ar ABU Zariya sun tafi yaji

A satin da ta gabata ne aka fito da wata jita-jitar mutuwar shugaban kasa, a inda wasu magoya bayansa ke maza fatan alheri.

Wadannan ne daga ciki dalilai da zai iya sa shugaba Buhari ya kara tsahon hutunsa:

1. Zai yiwu sakamakon gwajin asibiti

A wata sanarwar mai ba shugaban kasa shawara a kan labaru da kuma al’umma, Femi Adesina, ya bayyana cewa shugaban kasa ya gagara dawo domin ya na jiran sakamakon wasu gwaje-gwaje.

Femi Adesina ya bayyana cewa an shawarci shugaban kasar da ya kammala gwaje-gwajen kafin ya dawo kasar.

2. Rashin lafiyar shugaban kasa na iya zama mafi muni fiye da muke sani

Akwai jita-jita da yawa sun kewaye shugaba Buhari ta kiwon lafiya. Duk da yake mutanen da ke sukar gwamnatinsa suna kokawa cewa ba shida isashen lafiyan gudanar da mulkin kasan.

3. Matsayin Lai Muhammed

Ya kamata a tuna da cewa ministan bayani, al'adu da yawon shakatawa ya yi wa ‘yan Najeriya jawabi wasu kwanaki a baya a inda ya yi magana game da kiwon lafiyan shugaban kasa. Ya ce shugaban kasa ya bukaci tsaro fiye da kowa a kasa.

Yana mai tunatar da 'yan Nijeriya cewa fifita kiwon lafiya da kuma kare lafiya shugaban kasa a kowani lokaci dole ne da duk shugabanin kasashe.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa
NAIJ.com
Mailfire view pixel