Buhari bai da niyyar maida kasar nan ta musulunci - Lai Muhammad

Buhari bai da niyyar maida kasar nan ta musulunci - Lai Muhammad

Ministan watsa labarai, Lai Mohammed yace wannan gwamnati ba ta da wata shiri na boye ko ko a zahiri domin mai da kasa Najeriya kasar musulunci kawai

Lai Mohammed ya fadi hakanne a taron tattaunawa da mutane da akayi a garin Ilori, jihar Kwara

Buhari bai da niyyar maida kasar nan ta musulunci - Lai Muhammad

Buhari bai da niyyar maida kasar nan ta musulunci - Lai Muhammad

Lai Mohammed ya ce wannan zancen kanzon kurege ne kawai domin babu irin wannan magana ko mai kama dashi lissafin wannan gwamnati.

Ya kara da cewa ‘yan siyasa ne kawai suke amfani da irin wadannan kalamai domin ingiza mutane da tada zaune tsaye a kasa Najeriya.

Shugabannin addinin Kirista da yawansu sun zargi wannan gwamnati da kokarin mai da kasa Najeriya kasar musulunci.

Lai mohammed yayi kira ga ‘yan siyasa da su dai na amfani da addini domin cimma wata manufa nasu sannan malaman addinai suyi koyi da sarkin Musulmi Abubakar sa’ad da babban faston cocin Katolika da ke Abuja, Cardinal John Onaiyekan.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Cif Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Cif Obasanjo

Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel