Masu zanga zanga na son bata sunan Buhari ne – kungiyar Buhari

Masu zanga zanga na son bata sunan Buhari ne – kungiyar Buhari

Wani kungiyar matasa, magoya bayan Buhari, sun bayyana zanga zangan jiya a matsayin wani yunkuri da wasu mutane keyi don lalata shaharan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Masu zanga zanga na son bata sunan Buhari ne – kungiyar Buhari

A cewar kungiyar rahotannin rashin lafiya da kuma mutuwan shugaban kasa da zanga zangar da aka shirya na kin gwamnatinsa duk makarkashiya ce wanda ke son bata sunan shugaban kasar.

Sakataren kunyiyar na kasa, Success O. Success yace akwai wani makirci da yunkuri daga wasu kafofin watsa labarai na yanar gizo keyi a kan Buhari da gwamnatinsa.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta gargadi shugabannin addini kan kalaman tsokana

Ta bayyana cewa “Yayinda suka mai ma’ana keda kyau, wadanda keda mugun nufi suna halakarwa”.

“Zancen gaskiya shine cin hanci da rashawa ya zama tsutsa dake cinye ruhin kasarmu. Muna bukatan yaki da cin hanci da rashawa domin kwashe ginin da ya hana kasarmu ci gaba."

A cewar shugaban kungiyar, yayinda ake fama da wahalar rayuwa a kasar, gwamnatin tayi kokari sosai gurin dai-daita tattalin arziki da kuma dawo da farin ciki a fuskokin yan Najeriya. Sun nuna burin cewa tare da kasafin kudin 2017, gwamnatin Buhari na kan hanyan dawo da tattalin arzikin kasar kamar yadda take a da.

Domin karin bayani ku duba shafukanmu https://www.facebook.com/naijcomhausa/ da https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel