Gwamnatin tarayya ta gargadi shugabannin addini kan kalaman tsokana

Gwamnatin tarayya ta gargadi shugabannin addini kan kalaman tsokana

Gwamnatin Najeriya ta gargadi shugabannin addini da su guji yin furuci wanda zai iya kai ga rikicin addini.

Gwamnatin tarayya ta gargadi shugabannin addini kan kalaman tsokana

Gwamnatin tarayya ta gargadi shugabannin addini kan kalaman tsokana

Ministan bayanai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, wanda ya bayyana hakan a wani daki taro na arewa maso tsakiya a Ilorin yace akwai zargin cewa harkokin siyasa, kabilanci, rashin hakuri da ta’addanci sune abunda ke haddasa rikici tsakanin musulmai da Kiristoci.

Lai Mohammed ya kuma bukaci jaridun gida da na waje da su guji rahoton kawo jawaban shugabannin addini.

KU KARANTA KUMA: Ku gayyaci Goodluck jonathan don amsa tambayoyi, malaman Arewa ga hukumomin tsaro

“Ba tare da kame-kame ba, zan ce gwamnatin nan ta yi nasara da dama, duk da kalubalan da ta fuskanta tunda muka karbi mulki. Amma duk wani nasara da za’a samu zai zama mara ma’ana idan babu zaman lafiya.

“Kuma babu babban barazana ga zaman lafiya da hadin kai a kasarmu a yau sama da sakonnin addini na tsokana, siyasa da kuma shugabannin ra’ayi.”

“Irin wannan ru’danin kamar cewan ana so mayar da Najeriya kasar musulunci, Musulmai na kashe Kiristoci, bayyana Najeriya a matsayin guri mafi hatsari ga Kiristoci a duniya zai haddasa abu guda daya ne: hura wutan rikicin addini.

“Wadanda ke yin irin wadannan zage-zargen sun san cewa karya ne, amma sun rike addini a matsayin wani makami na hargitsa gwamnatin yau, dauke hankulan mutane daga yaki da cin hancin da rashawa da gwamnati keyi da kuma gida tashin hankula mara ma’ana."

Ya kara da cewa hukumar sojojin kasar ba ita ke ba Fulani makiyaya makamai don su kashe kiristoci ba.

Domin karin bayani ku duba shafukanmu https://www.facebook.com/naijcomhausa/ da https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa
NAIJ.com
Mailfire view pixel