Ku gayyaci Goodluck jonathan don amsa tambayoyi, malaman Arewa ga hukumomin tsaro

Ku gayyaci Goodluck jonathan don amsa tambayoyi, malaman Arewa ga hukumomin tsaro

- Wasu malaman Arewa sun yi Allah wadai da furucin da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi a kan rikicin dake gudana a yankunan

- Malaman sunce sanarwan da Jonathan yayi a makon da ya gabata a wani taro tare da United State congress a kan rikicin addini dake yankin Arewacin kasar ya kasance ganganci da rashin kulawa

- Sun kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su gayyaci tsohon shugaban kasa don amsa tambayoyi

Ku gayyaci Goodluck jonathan don amsa tambayoyi, malaman Arewa ga hukumomin tsaro

Wasu malaman Arewa sun yi Allah wadai da furucin da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi a kan rikicin dake gudana a yankunan

Malaman sunce sanarwan da Jonathan yayi a makon da ya gabata a wani taro tare da United State congress a kan rikicin addini dake yankin Arewacin kasar ya kasance na ganganci da rashin kulawa.

Da yake magana da yan jarida a Abuja a ranar Litinin, 6 ga watan Fabrairu, shugaban yankin arewa ta tsakiya Musa Fomson ya bukaci hukumomin tsaro da su gayyaci tsohon shugaban kasa don amsa tambayoyi.

KU KARANTA KUMA: Babu abunda zai dakatar da Arewa da Buhari a 2019 – Sani

Fomson yace gayyata da tambayan Jonathan zai ba hukumomin tsaro daman sanin niyansa a kan Najeriya.

Yace Jonathan yaki sanar da masu sauraronsa na Amurka cewa makiyaya masu kashe-kashe bazasu kai matsayin kungiya masu hadari na hudu a duniya ba inda ace shi da mataimakansa basu sace kudin da yakamata ayi amfani dashi gurin siyan makamai don yakar yan kungiyar Boko Haram ba.

Yaci gaba da daura laifin matsin rayuwar da yan Najeriya da dama ke fuskata a kasar kan tsohon shugaban kasa.

“Idan da gaske Goodluck Jonathan na son Najeriya, dole ne ya daina dukkan ayyukansa na batanci kamar irin furucin da yayi agaban majalisar Amurka inda ya taka rawar gwamnati mai ci ta hanyar tataunawa da masu shiga tsakani na Amurka.

“Dole yayi magana da dukkan yan ‘koransa kan su dawo da dukka kudaden da suka sata daga Najeriya, imma na kudin siyan makamai, wanda aka sata daga kudin danyen mai ko kuma bashin waje da suka karkatar zuwa aljihunsu.”

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel