Likitocin Asibitin Jami’ar ABU Zariya sun tafi yaji

Likitocin Asibitin Jami’ar ABU Zariya sun tafi yaji

– Likitoci sun shiga yajin-aikin a Asibitin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya

– Yajin aikin ya shafi sauran Malaman Asibiti

– Ma’aikatan sun ce babu ranar dawowa

Likitocin Asibitin Jami’ar ABU Zariya sun tafi yaji

Likitocin Asibitin Jami’ar ABU Zariya sun tafi yaji

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Malaman Asibitin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya sun shiga wani yajin aiki jiya. Kwanan ne dai aka sake bude Asibitin bayan an kaddamar da wasu gina-gine an kuma canza masa suna.

Ma’aikatan dai wanda suka hada da Likitoci da sauran Malaman Asibiti sun tafi yajin ne a jiya wanda kuma suka ce babu ranar dawowa har sai Hukuma ta duba kukan su. Ma’aikatan dai sun ce Hukumar Jami’ar ta gaza biya masu bukatun da suka yi yarjejeniya.

KU KARANTA: Takaitattun labarai a yau

Shugabannin Kungiyoyin Ma’aikatan Asibitin guda hudu dai suka rattaba hannu a kan takardar da ke sanar da cewa Ma’aikatan Asibitin za su koma yajin aikin su. Wani ya bayyana mana cewa ya je Asibitin amma ba a aiki dole ta sa ya dawo gida. Har yanzu dai Jami’ar ba tace uffan ba.

Haka dai kwanaki Likitocin Asibitin koyan-aiki na Jami’ar dai ta Ahmadu Bello suka shiga yajin-aiki na din-din-din. Kungiyar Likitocin Asibitin da ke Shika, sun shiga yajin aikin ne bayan an gaza biya masu bukatun su.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel