Ku kara hakuri da mu-Inji Bola Tinubu

Ku kara hakuri da mu-Inji Bola Tinubu

– Jigo a Jam’iyyar APC ya aika sako ga masu zanga-zanga

– Bola Tinubu ya roki Jama’a su kara hakuri

– Tinubu yace ya san Jama’a na cikin wani hali na ka ni-ka yi

Ku kara hakuri da mu-Inji Bola Tinubu

Ku kara hakuri da mu-Inji Bola Tinubu

A jiya ne aka gudanar zanga-zanga ga Gwamnatin Buhari saboda halin da ake ciki a Kasar a halin yanzu. Wani Babban Jigo na Jam’iyyar APC mai mulki Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yayi kira ga ‘Yan Najeriyan da su kara hakuri.

Masu zanga-zangar sun dura gidan Asiwaju Tinubu a Legas inda suka nemi ya fito yayi bayani ga Jama’a. Daga baya dai Bola Tinubu ya fito inda ya kara ba Jama’a hakuri. Tinubu yace tabbas sun sa ana cikin halin ni-‘ya su a Najeriya. Tinubu yace ba zai hana mutane zanga-zanga ba don su ma da haka suka fara.

KU KARANTA: Ana kuka a mulkin Buhari

Bola Tinubu yace shekaran wannan Gwamnati biyu da kafuwa ya kuma nemi ‘Yan Kasar su kara hakuri tare da sa rai. Masu zanga-zangar sun koka game da sha’anin rashin aikin yi da sauran su. Tinubu yace Najeriya ta shiga wani hali ne saboda barnar da aka yi a baya.

Haka kuma rikici na nema ya barke a Jam’iyyar APC, dama can an dade ana ta bugawa tsakanin Injiniya Kwankwaso da kuma Gwamna mai-ci na Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Yanzu ta kai an samu sabani tsakanin mataimakin shugaban Jam’iyyar na Yankin Arewa Inuwa AbdulKadir da kuma Ma’ajin Jam’iyyar na Kasa watau Bala Gwagwarwa.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu

Yadda neman gira na hauren baki a kasar Libya yake janyo musu asarar idanu
NAIJ.com
Mailfire view pixel