Babachir zai bayyana gaban Sanatoci

Babachir zai bayyana gaban Sanatoci

– Sakataren gwamnatin tarayya zai bayyana a gaban Sanatoci

– Babachir Lawal zai yi bayani game da kasafin kudin bana ga Majalisar

– Kasafin Ofishin Sakatare Babachir ya haura gaba bana

Babachir zai bayyana gaban Sanatoci

Babachir zai bayyana gaban Sanatoci

Sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal zai bayyana a gaban Sanatocin Najeriya inda zai kare kasafin kudin bana na Ofishin sa wanda ya kusa kai Naira Biliyan 10, a ciki dai har da kudin da za a sayawa tsofaffin shugaban kasa sababbin motoci.

Ofishin Sakataren gwamnatin ya kuma ware sama da Biliyan 2 domin wasu ayyuka. Babachir ya koka da cewa Ofishin na sa bai samu wani kudi ba a bara watakila hakan ta sa kasafin kudin bana ya kara yawa.

KU KARANTA: FFK ya nemi sauki a Kotu

Babachir zai bayyana gaban Sanatoci

Babachir zai bayyana gaban Sanatoci

Sanata Suleiman Hunkuyi wanda shine mataimakin Kwamitin yace za a duba maganganun na Babachir, sannan kuma ya yabawa Gwamnati da kokarin da tayi wajen sakin kudi bana. Watakila kuma Majalisar za ta nemi ganawa da Ministan kasafi da na tattalin arzikin kasa.

Osinbajo yayi doguwar waya da Muhammadu Buhari ya kuma bayyanawa ‘Yan Jaridan da ke Fadar shugaban kasar abin da suka tattauna a wayar. Osinbajo yace sun tattauna ne game da tattalin arzikin kasa da kuma batun kasafi da Buhari, yace Buhari na so ya ji inda aka kwana.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel