Abin da na tattauna da Buhari a waya-Osinbajo

Abin da na tattauna da Buhari a waya-Osinbajo

– Shugaban kasa na rikon-kwarya Osinbajo yayi doguwar waya da Muhammadu Buhari

– Osinbajo ya sanar da Buhari cewa ana zanga-zanga

– Buhari na cikin koshin lafiya Inji Mataimakin Sa

Abin da na tattauna da Buhari a waya-Osinbajo

Abin da na tattauna da Buhari a waya-Osinbajo

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kara tabbatar da cewa Muhammadu Buhari na nan cikin koshin lafiya. Osinbajo yace kuma Buhari zai dawo Najeriya yana kammala gwajin da yake yi a asibiti.

Osinbaji yayi doguwar waya da Muhammadu Buhari ya kuma bayyanawa ‘Yan Jaridan da ke Fadar shugaban kasar abin da suka tattauna a wayar. Osinbajo yace sun tattauna ne game da tattalin arzikin kasa da kuma batun kasafi da Buhari.

KU KARANTA: Mun ji kukan ku 'Yan Najeriya

Mukaddashin shugaban kasa Osinbajo yace ya kuma fadawa Buhari cewa ana zanga-zanga a kasar inda mutane ke kuka musamman game da tattalin arziki. Sannan kuma dai Osinbajo yayi watsi da rade-radin cewa ana nema a tursasa ya sauka daga kan kujera, yace babu wanda ya isa.

A jiya ne aka gudanar zanga-zanga ga Gwamnatin Buhari saboda halin da ake ciki a Kasar a halin yanzu. Wani Babban Jigo Jam’iyyar APC mai mulki Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yayi kira ga ‘Yan Najeriyan da su kara hakuri.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel