Shekaru hudu ku ka zabe mu ba biyu ba Inji Amaechi

Shekaru hudu ku ka zabe mu ba biyu ba Inji Amaechi

– Ministan Sufuri Rotimi Amaechi yace kusan an kammala nemo bashin gina hanyar jirgin kasa

– Gwamnatin tarayya za ta gina hanyar jirgin kasa Legas zuwa Kano a kan Dala Biliyan $7.5

– Yanzu Majalisa kadai ake jira ta amince da karbo bashin

Shekaru hudu ku ka zabe mu ba biyu ba Inji Amaechi

Shekaru hudu ku ka zabe mu ba biyu ba Inji Amaechi

Ministan Sufuri na Najeriya Rotimi Amaechi yace yanzu haka kusan an kammala nemo bashin da za a gina hanyar jirgin kasa na Legas zuwa Kano. Amaechi ya bayyana haka ne a wani taro da Gwamnatin tarayya tayi a Ilorin.

Rotimi Amaechi yace an samo bashin ne a Bankunan Kasar China, sai dai yanzu abin da kawai ya rage Majalisa ta amince a karbo kudin. Ginin hanyar jirgin kasar daga Ibadan zuwa Ilorin zuwa Minna sannan a shiga Kaduna sai a isa Kano zai ci sama da Dala Biliyan 6. Karashen aikin zai ci sama da kuma Dala Bilyan guda.

KU KARANTA: Takaitattun labarai a wannan mako

Amaechi ya bayyana wasu ayyuka da za a kammala wannan shekarar yake cewa don haka a jira sai nan da shekaru hudu sai a duba ayyukan da Gwamnatin Buhari tayi ba yanzu ba da ba a ko wuce shekaru biyu ba.

A jiya ne aka gudanar zanga-zanga ga Gwamnatin Buhari saboda halin da ake ciki a Kasar a halin yanzu. Wani Babban Jigo a Jam’iyyar APC mai mulki Bola Tinubu yace shekaran wannan Gwamnati biyu da kafuwa ya kuma nemi ‘Yan Kasar su kara hakuri tare da sa rai.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

NAIJ.com
Mailfire view pixel