Takaitattun labaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Kamar yau da kullun, jaridar NAIJ.com tanan kawo muku Takaitattun labaran abubuwan da suka faru karshen makon da ya gabata a fadin Najeriya. Ku sha karatu

1. ‘Yan Boko Haram sun kwace wata gari a Yobe

Takaitattun labaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Takaitattun labaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Wasu mambobi kungiyar yan tada kashin bayan Boko Haram sun kwace garin Sasawa, wata gari a jihar Yobe da suka far ma bayan musayan wuta da rundunar sojin Najeriya a ranan Lahadi, 5 ga watan Febrairu.

2. Mara imani ne ke fatan mutuwan Buhari – Kakakin APC

Takaitattun labaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Takaitattun labaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Tsohon ministan wasa da matasa kuma kakakin jam’ iyyar APC, Mallam Bolaji Abdullahi, yace rashin imani ne mutum ya dinga fatan shugaba Buhari yam utu.

3. Karen EFCC ya biyo James Ibori da laifuka 170

Takaitattun labaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Takaitattun labaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC tana shirya damke tsohon gwamnan jihar Delta bayan ya kwashe shekaru 6 a kurkukun kasar Ingila.

4. Hukumar ‘yan sanda ta gano mabuyan ‘yan Boko Haram a jihar Kano, ta damke mutane 53

Takaitattun labaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Takaitattun labaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Hukumar yan sandan ta gano hakan ne a wata farmaki da ta kai tare da hukumar tsaron farin hula wato Nigerian Securities and Civil Defence Corps, da hukumar Hizbah da kuma yan banga a jihar.

5. EFCC ta karbe gidan wani tsohon Gwamna

Takaitattun labaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Takaitattun labaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta karbe wasu kaya na tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Isa Yuguda. Wannan ya biyo bayan wani babban Kotun tarayya da ke Abuja ta ba Hukumar damar hakan.

6. El-Rufai da Buratai sun shimfida harsashin samar da zaman lafiya mai dorewa

Takaitattun labaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Takaitattun labaran abubuwan da suka faru ranan Litinin

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai tare da babban hafsan sojojin kasa Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai sun kafa harsashin gina bataliyar sojoji a ranar Asabar 4 ga watan Fabrairu don tabbatar da tsaro a kudancin jihar Kaduna.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hayayyafar da muke yi tayi yawa, nauyi ne babba a gobe - Obasanjo

NAIJ.com
Mailfire view pixel