Rikici ya barke a Jam'iyyar APC

Rikici ya barke a Jam'iyyar APC

– Rikicin Kwankwaso da Gwamna Ganduje ya hafa fada a APC

– Sabanin Gwamnan da tsohon mai gidan sa ya shiga tsakanin wasu manyan APC

– An sabu sabani tsakanin mataimakin shugaban Jam’iyya da Ma’aji

Rikici ya barke a Jam'iyyar APC

Rikici ya barke a Jam'iyyar APC

Rikicin APC na Jihar Kano ya fara shafan Jam’iyyar a mataki na kasa. An dai dade ana ta bugawa tsakanin tsohon Gwamnan Jihar Kano Injiniya Kwankwaso da kuma Gwamna mai-ci Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Yanzu dai kamar yadda muka samu labari daga Jaridar Daily Trust har ta kai an samu matsala tsakanin mataimakin shugaban Jam’iyyar na Yankin Arewa Inuwa AbdulKadir da kuma Ma’ajin Jam’iyyar na Kasa watau Bala Gwagwarwa.

KU KARANTA: Gwamna Ay Fayose ya cika baki

Gwagwarwa ya rubuta wasika ga Shugaban Jam’iyyar na Kasa Cif Oyegun inda yake nema a sake duban lamarin rikicin Jam’iyyar a Jihar Kano. An dai tunbuke Shugaban Jam’iyyar Umar Doguwa da wasu ‘Yan Kwankwasiyya aka maye guraben su da masu goyon bayan Gwamna mai-ci Abdullahi Ganduje.

Haka kuma Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo yace duk wanda bai son shugaba Buhari ya jira zabe mai zuwa a shekarar 2019 sai ya zabi wani Dan takara na dabam. Obasanjo yace ba daidai ba ne fatan mutuwa ga shugaban.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa da kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel